Biyo bayan wani tashin bam da ya afku a sansanin 'yan gudun hijira da ke Malkohi wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama, lamarin ya kara tada hankalin 'yan gudun hijirar.
Kasashen Rasha da Angola sun takawa kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya akan Sudan ta Kudu birki
Jeremy Corbyn wanda da farko ba a zaci zai c kai labari ba, lokacin da ya tsaya takarar shugabancin jam’iyar Labor a Birtaniya ya lashe zabe
mataimakiyar sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace ba za a dage takunkumin da aka sawa Rasha ba sai an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan rikicin Ukrraine baki daya.
Jam'iyar PDP da ta sha kaye a jihar Bauchi ta dauki matakin gyara kura kurai da tace an tafka da ya janyo mata faduwa zabe bara,. Ta kuma sauke wadansu shugabannin jam'iyar tare da barazanar kaisu gaban hukumar EFCC
Hukumomin kasar Somaliya sunce yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab sun kwace wasu birane guda biyu a kudancin kasar a jiya Asabar bayan da sojojin kungiyar kasashen Africa da ake cewa AMISOM a takaice sun janye daga biranen.
Jam’iyar UDR Tabbat ta jamhuriyar Niger ta maida martani akan matakin korar ‘yan jam’iyar daga gwamnatin shugaba Yusufu Mahammadu ba tare da an shawarci shugabannin jam’iyar ba.
A wani yunkurin sausauta zaman tankiya ko kuma zaman dar dar akan caje cajen ta'adanci da kuma gano hanyoyin inganta yunkurin samun zaman lafiya na Afghanistan, jiya Juma'a shugaban kasar Afghanistan da wani baban jami'in Pakistan makwapciyarta suka yi shawarwari a birnin Kabul.
Shugaba Vladimr Putin na kasar Rasha yace kasar sa tana son ta kafa wani shirin kawancen kasa da kasa na yaki da ta'adanci.
Shugaba Barack Obama yace Amirka da kasar Saudi Arabiya zasu ci gaba da hada kai wajen kokarin dakile aiyukan ta'adanci a gabas ta tsakiya da duniya ga bakin dayanta ciki harda yaki da ake fafatawa da yan yakin sa kan kungiyar Islamic State.
Kwamitin kula da wadanda suka rasa matsugunansu sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram yAce an kashe naira biliyan uku daga cikin naira biliyan ishirin da biyar da gidauniyar ta sami karbowa daga cikin naira biliyan hamsin da hudu da aka yiwa gidauniyar alkawari
Domin Kari