WASHINGTON, DC —
Wannan ya biyo bayan shigar da karar da uwar jam’iyyar PDP tayi, akan matakin da ‘yan majalisar suka dauka na canza sheka.
Awwalu Abba dan kwamitin zartaswa ne, na PDP yace “to idan har kotu, da INEC zasu ce basu shaida wata jam’iyya ba sai wannan, ashe kuwa dan majalisa idan yace ya bar wannan jam’iyya, yace ya koma wata jam’iyya to wajibi ne a kundun tsarin mulki ya sauka daga kan kujerarsa.
Sai dai shugaban sashen bincike da nazari, na jam’iyyar APC mai adawa, Dr. Garba Abadi yace zasu daukaka kara. Yace “zamu daukaka kara har sai munga abunda ya turewa buzu nadi.”
Dr. Abadi ya kara da cewa “kafin ayi kamar wannan, an sha yi a baya, wannan karo, bita da kulli ake so a yi mana”.
Da alamu wannan dambarwar zata ja tsawon watanni. Idan ba’a manta ba, akwai ‘yan majalisar dattawa 11 na PDP da suka koma APC.