Wasu masu sharhi na ganin rashin baiwa mataimakin shugaban kasa daman rike kasar yayin da shugaban ke duba lafiyarsa a Ingila, ka iya shafar dangantakarsu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da hafsoshin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro na Najeriya gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa London don gain likita.
Gwamnatin Nigeria ta ba da umurnin hana hakar zinari da sauran albarkatun ‘kasa a jihar Zamfara tare da haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar A kokarin yaki da ta’ adds ci ya yayi kamari a jihar.
Gwamnonin arewacin Najeriya sun dukufa wajen neman hadin kan gwamnatin tarayya, don kafa rugage da wuraren kiwo domin hana Fulani yawon kiwo da ke sanadin tashe tashen hankula.
Najeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen tsananta matakan dakile yaduwar cutar corona, yayin da ita kuma cutar ke kara barazana tare da neman rikida a wasu kasashen.
Biyo bayan ceto daliban makarantar sakandaren garin Kankara da aka yi bayan da aka sace su a 'yan kwanakin da suka gabata, yanzu hankali ya koma akan yadda kwararru zasu taimaka wa daliban warwarewa da matsalar fargaba da firgita.
A daidai lokacin da Majalisar Wakilan Najeriya ke jiran bayyanar shugaban kasa gabanta yau Alhamis, domin amsa tambayoyi game da halin tabarbarewar tsaro da kasa ke ciki, Ministan Shari’a ya ce bayanin Buhari ga Majalisa na iya amfanar ‘yan bindiga
A cigaba da lalubo mafita game da matsalolin tsaro da rayuwa a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki, inda ya ciza ya kuma hura.
Yayin da Najeriya ke bukin zagayowa ta 60 ta ranar samun 'yancin kanta a cikin wani yanayi na matsalolin tsaro, tattalin arziki da kuma annobar COVID-19, Shugaba Buhari ya ce muddun aka hada kai za a kai ga gaci.
Shugaban kwamitin Shugaban Nigeria Mai binciken badakalar da ake zargin Mustafa Ibrahim Magu ya tafka a hukamar yaki da cin hanci da rashawa, Justice Ayo Salami ya karyata labarin da lauyoyin Magu suka yada na cewar wai yayi nadamar kar’bar aikin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake yi wa ‘yan kasa bayani akan matakan da mahukuntan kasar da jami’an kiwon lafiya za su dauka domin hana bazuwar cutar coronavirus da ta kama sama da mutane dubu yayin da fiye da arba’in suka mutu.
Rahotan da kungiyar fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa Transparency International ta fitar a kan Najeriya, na nuni da cewa an samu karuwar cin hanci da rashawa maimakon raguwarsa.
Najeriya ta samu ‘yancin cin gashin kai ranar 1 ga watan Oktoban 1960, daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya.
A wani mataki mai kama da tauna tsakuwa da kuma ishara ga baragurbin jami'an gwamnati, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rusa kwamitin binciken tafka almundahana saboda wani abu mai kama da baiwa kura ajiyar nama.
Domin Kari