Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Buhari Na Ranar Samun 'Yancin Kai: Najeriya Za Ta Kai Ga Gaci


Shugaba buhari
Shugaba buhari

Yayin da Najeriya ke bukin zagayowa ta 60 ta ranar samun 'yancin kanta a cikin wani yanayi na matsalolin tsaro, tattalin arziki da kuma annobar COVID-19, Shugaba Buhari ya ce muddun aka hada kai za a kai ga gaci.

Yau an yi bukukuwan cikar Nigeria shakaru 60 da samun yancin kai daga mulkin mallakar kasar ingila, kamar yadda aka saba yi kusan a duk zagayowar wannan rana. Shugaba Buhari ya kwashe kimanin minti 20 ya na jama’ar kasar jawabi game da tarihin wannan kasar bakar fata mafi girma da inda aka fito da inda ake a halin yanzu da kuma inda ake fatan kaiwa.

Buhari ya tabo batutuwa da dama: kama daga nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta samu zuwa bukatun ‘yan kasa musamman na tsaro, tattalin arziki da kuma hadin kai – kai har ma da bukatun jama’a na yau da kullum – kamar yadda ya fahimce su a matsayinsa na Shugaban kasa kuma ya ke aiki a kansu.

Buhari Wurin Bukin Zagayowar Ranar 'yancin Kai
Buhari Wurin Bukin Zagayowar Ranar 'yancin Kai

Buhari na tabo matsalolin da ke da nasaba da wannan marra ta annobar COVID-19, wadda ya ce ta durkusar da tattalin arzikin kasashen duniya da rayuwar al’umma gaba daya ciki har da ba Najeriya.

“Abin da zan ce a takaice, game da inda mu ka kai a halin yanzu a matsayin kasa, shi ne ya wajaba mu shata inda ya kamata mu dosa yadda ya kamata da kuma yadda za mu iya zuwa tare. Yau ina mai sane da cewa tattalin arzikinmu da na sauran kasashen duniya ya durkushe; akwai kuma matsalolin tsaro a wasu yankunan kasarmu a yayin da jama’armu ke fuskantar wasu matsalolin kuma na rayuwa masu nasaba da siyasa.”

Hotunan Bukin Zagayowar Ranar 'Yancin Kai
Hotunan Bukin Zagayowar Ranar 'Yancin Kai

Buhari ya kara da cewa hatta bangaren ayyukan gwamnati kamar na ‘yan sanda da sojoji da fannin shari’a da dai sauransu duk na fuskantar babban kalubale ta yadda ya zama dole Najeriya ta dau matakin gyara su don kasar ta samu cigaba.

Shugaban na Najeriya ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su bayar da muhimmanci ga batun hadin kai da warware matsaloli masu nasaba da kyama ko tsanar juna haka siddin, da matsalar nuna banbancin addini da na kabilanci da sauran bangarorin rayuwa da ake samun kalubale matuka. Ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su daina ganin kansu a matsayin ‘yan wani bangare kafin su ga kansu a matsayin ‘yan Najeriya. Ya ce muddun aka samu hadin kai to labudda za a kai ga gaci.

Sojojin kasar dai sun burge jama’a da irin fareti da kuma shawagin jiragen sama da su ka yi.

Ga Umar Faruk Musa da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG