A Indiya masu zanga-zanga magoya bayan Ram Rahim Singh, sun fara tafiya gidajensu domin kawo karshen jan daga da sojoji.
Rundunar sojin kasar Lebanon ta sanar da tsagaita wuta a yaki da mayakan IS a kan iyakar Syria.
Kungiyar Tarayyar Turai na duba yiwuwar dakatar da daukar nauyin manyan ayyukan bunkasa rayuwa a kasashen da bakin haure ke fitowa zuwa Turai.
Jiya Jumma’a Amurka ta haramta duk wata huldar kasuwanci da Venezuela a yunkurin Washington na baya bayan nan, na matsawa gwamnatin shugaba Nicolas Maduro lamba.
A birnin Jos, an kaddamar da gidauniyar marigayi Alhaji Adamu Dan Maraya Jos, inda aka bayyana kyawawan darusa da wakokin marigayin ke da su, da kuma halayan marigarin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 23 ga watan Agusta domin tunawa da cinikayyar bayi da kuma haramta bauta a duniya.
Kwamitin da mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osibajo ke jagoranta ya mikawa shugaban kasa rahotan cikakken binciken da ya gudanar na zargin wata badakala da ake yiwa sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar da Ambasada Ayo Oke.
Wani sabon rikici ya sake barkewa a jam’iyar APC reshen jihar Taraba yayin da tsohon mukaddashin gwamnan jihar Garba Umar UTC, ke sauya sheka zuwa jam’iyar.
Noma Tushen Arziki
Kasar Iraq ta kaddamar da wani farmaki yau Lahadi da safe da nufin sake kwace Tal Afar, wani gari dake gabashin Mosul, daga hannun mayakan IS.
Dubban Amurkawa ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da zanga-zangar fadin albarcin baki da masu ra'ayin 'yan mazan jiya suka yi.
An gudanar da bikin jana’izar tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.
A yau Asabar shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya sauka a birnin Abuja, bayan Kwashe sama da watanni uku yana jinya a birnin London dake Burtaniya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja babban birnin kasar bayan doguwar jinya a London inda yayi jinyar wata cuta da ba a bayyana ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 19 ga watan Agusta a matsayin ranar tausayawa Bil Adama a fadin Duniya.
Mai yiwa ne an kashe direban da motar da ya kai hari ya kashe mutane a birnin Barcelona ranar Alhamis.
Domin Kari