Jami’an fafutukar yaki da bauta a jamhuriyar Nijar sun nuna damuwa a game da wasu matsalolin dake maida hannun agogo baya wajen kawar da wannan dabi’a daga yankunan da wasu attajirai da masu bakin fada aji ke mayar da mutane bayu duk kuwa da cewa doka ta haramta bauta a Nijar.
Imani akan wasu abubuwan dake da nasaba da al’adu na kan gaban dalilan da aka gano cewa suna kawo cikas a yaki da bauta a jamhuriyar Nijar. duk kuwa da shekarun da aka kwashe hukumomi da kungiyoyi suna gwagwarmayar hadin gwiwa akan wannan matsala.
Mallam Danbaji Son Allah, memba a kwamitin kasa mai yaki da bauta, cewa ya yi har yanzu ana fuskantar matsalar bauta, kasancewar rashin fahimta da mutane ke yiwa bauta.
Bisa la’akari da yadda wasu mutane suka yi zurfi wajen mayar da kansu tamkar bayi ko kuma mallakin wani da sunan bauta, matsa kaimi akan ayyukan fadakarwa ya zama wajibi ga masu yaki da bauta.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma daga jamhuriyar Nijar.
Facebook Forum