An shafe daren jiya a Najeriya ana yayata jerin sunayen wadanda ake cewa, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ke shirin zaba a matsayin Ministoci, a kafofin sada zumunta na yanar gizo duk da yake babu wata majiya a hukumance da ta tabbatar da haka.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta ce cire tallafin fetur ba tare da matakan rage radadi ga talakawa ba zai jefa akasarin jama'a cikin karin kuncin talauci.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce za ta cigaba da hukunta duk jam'ian ta da ta samu da laifi a lokacin gudanar da babbar zaben 2023 da ya gabata.
Biyo bayan sauke akasarin manyan jami'an tsohuwar gwamnatin da ta shude ta Buhari, yanzu hankali ya koma kan nada majalisar zartarwa ta sabuwar gwamnatin Bola Tinubu.
A wani taron da aka yi a Bauchi, matasa sun ci gaba da tattaunawa kan abun da ya dace su maida hankali a kai bayan kammala babban zaben Najeriya na 2023.
A ranar Jumma'a jami'ai sun baiyana cewa 'yan ta'adda a arewa maso gabashin Najeriya sun yi kisan gilla ga manoma takwas, tare da sace wasu 10.
Shirin zauren matasa a wannan makon, ya yi bayani kan wani taro da aka yi a jihar Bauchi, inda matasa su ka tattauna kan abin da ya dace su (matasa) maida hankali a kai bayan kammala babban zaben Najeriya na 2023.
Shirin Zauren Matasa har yanzu muna Bauchi ne inda matasa su ka taru suka tattauna abin da ya da ce matasa su maida hankali a kai bayan kammala babban zaben Najeriya na 2023.
Sirika ya maida martani ne kan caccakar da ya sha bayan gabatar da jirgi da ke dauke da tambarin Nigeria Air da aka gano shatar sa a ka yi daga kamfanin jirgin Ethiopia da yi masa fenti.
Kayan masarufi da kudin sufuri sun yi tashin gauron zabi sanadiyyar janye tallafin man fetur da Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya sanar ranar da ya dauki rantsuwa, yanayin da ya sa farashin ya cira da kusan kashi 200%.
Sabon shirin arewa a yau zai duba sanya hannu kan dokar kafa hukumar kula da almajirai da tsohuwar gwamnatin Buhari ta yi a jajiberin sauka daga mulki, da kuma matakan kula da daliban jihar Yobe da su ka dawo daga Sudan don guje wa fitina.
Sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara jan ragamarsa da soke tallafin man fetur, baya ga wasu jerin alkawura da ya yi.
Shin wadanda su ka lashe zabe za su cika alkawarin kyautata rayuwar matasa ko sun yi zane kan ruwa ne, matasan sun duba matakan dogaro da kai maimakon jiran gawon shanu.
An tsaurara matakan tsaro a Abuja gabanin rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban kasa ranar Litinin mai zuwa.
Domin Kari