Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AREWA A YAU: Matakan Da A Ke Dauka Kan Dawo Da Daliban Jihar Yobe Gida Daga Sudan Kashi Na 2 - Yuni 7, 2023


Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin arewa a yau zai duba sanya hannu kan dokar kafa hukumar kula da almajirai da tsohuwar gwamnatin Buhari ta yi a jajiberin sauka daga mulki, da kuma matakan kula da daliban jihar Yobe da su ka dawo daga Sudan don guje wa fitina.

Akwai kimanin yara miliyan 13 da ke ragaita kan titunan arewacin Najeriya, ko dai da sunan bara ko kuma iyayen su ba sa iya daukar nauyin su.

Dan majalisar dokoki Shehu Balarabe Kakale daga Sokoto, ya jagoranci tsarawa da samar da dokar da tsohon shugaban kasa Buhari ya sa mata hannu.

Shirin ya kuma dora daga inda ya tsaya a makon jiya inda mai kula da tura dalibai karatu zuwa kasashen Larabawa daga jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ya ci gaba da bayani kan bin kadin daliban da rikicin Sudan ya tilasta su ka dawo gida.

Saurari shirin cikin sauti:

AREWA A YAU: Matakan Da A Ke Dauka Kan Dawo Da Daliban Jihar Yobe Gida Daga Sudan Kashi Na 2 - Yuni 7, 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:26 0:00

XS
SM
MD
LG