Yayin da ma'aunin tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 27.33% bisa rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya, masana sun ba da shawarar komawa kan kananan sana'o'i don samun mafita.
Hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC da TUC ta ayyana tsunduma gagarumin yajin aiki daga ranar Talatar nan ne har sai baba ta gani.
Hukumar raya Babban Birnin Tarayya na Abuja ta ce sam ba kamshin gaskiya a labarin da aka yi ta yayata a kafafen sada zumunta cewa Ministan birnin Nyesom Wike zai rushe wani sashen babban Masallacin tarayya da ke Abuja.
Jakadan Falasdinu a Najeriya, Abdullah Shawesh, ya ce cikin wadanda ke gwagwarmayar kwato wa Falasdinawa hakkinsu akwai mabiya addinin kirista da ma Yahudawa.
Rahotanni sun ce 'yan fashin sun kwashe sama da sa'a guda suna sata a bankuna kafin daga bisani su arce.
Lauyoyi da masu sharhi kan lamuran siyasa na mara baya ga dawo da shari'un karar zaben 2023 ga kotun daukaka kara ta Abuja da Legas.
Ma'aikatan hukumar yi wa kamfanoni rajista ta Najeriya "Corporate Affairs Commission" sun yi gangamin nuna farin cikin rashin sabuntawa shugaban hukumar Barista Garba Abubakar sabon wa'adi bayan shafe shekara uku da wata tara kan kujera.
Farashin litar man fetur kan iya karuwa a ko yaushe; hakanan ba mamaki a wayi gari da dogayen layukan neman fetur don barin kasuwa ta daidaita kanta.
Gwamnatin ta Najeriya ta dakatar da Ziyarar ne har sai an samu salama, biyo bayan kaurewar fada tsakanin Falasdinawa ‘yan kungiyar Hamas da sojojin Isra’ila.
Masu sharhi kan fitinar da ta barke tsakanin Isra'ila da 'yan Hamas na karfafa tunanin cewa Majalisar Dinkin Duniya ce ke da hakkin shiga tsakani don kawo karshen wannan yaki da samun zaman lafiya.
Domin Kari