Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki kalilan gabanin manyan tarukan jam’iyyun a karshen watan nan don fidda ‘yan takarar.
A jam’iyyar APC mai mulki a taraiya da ke da kimanin ‘yan takara 30, a na ganin ‘yan takarar da su ka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da uban jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu na zaga jihohin da su ka fi yawan kuri’u.
Jigon APC Ibrahim Masari da ke mara baya ga Tinubu na cewa Osinbajo ba zai taka mu su birkin samun kai wa ga gaci ba duk da kasancewar sa a fadar Aso Rock.
PDP da ke adawa na yunkurin hada kan ‘yan takarar ta da su ka hada da gwamnoni, manyan jami’an gwamnati da su ka yi fice da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a gefe guda.
Magoya bayan Atiku na nuna shi kadai zai iya yi wa APC zarra a zaben yayin da wasu ke cewa ya dace a gwada wani sabon dan takara.
Gwamna Bala Muhammad na Bauchi na cikin gwamnonin da ke takarar, ya na mai cewa su na da hikimar dawo da Najeriya kan turbar arziki.
Sauran jam’iyyun adawa na nuna za su iya ja da manyan guda biyu matukar jama’a su k adage don kawo sabon canji.
Manjo Hamza Almustapha da ya tsaya a jam’iyyar AA na cewa alamun jam’iyyar kadai sun isa nuna kyakkyawar alkibla.
Hukumar zabe ta tsaida ranar 3 ga watan gobe a matsayin ranar da jam'iyu za asu mika sunayen ‘yan takarar shugaban kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: