Yaran da suka rasa iyayensu a rikicin boko haram, a gabashin arewacin Najeriya da wasu daga Sokoto sun kwashe shekaru biyar suna samun kulawa a dukkannin bangarorin rayuwa, daga neman ilimi daga matakin firamare har zuwa jami'a da kuma bangaren koyon sana'o'in hannu.
Samun ‘yantar da dalibai mata hudu daga cikin sauran goma sha daya ‘yan makarantar birnin Yauri da suka rage a hannun masu garkuwa da mutane, alama ce da ke nuna ana iya kubutar da sauran daliban.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli Akan Al'amuran Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.
Jami’in tattara sakamakon zabe ya ayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu.
A mafi yawan rumfuna, an samar da isassun jami'an tsaro kuma sun kula da yadda al'amurra suka gudana yayin zaben.
Masu zabe a Najeriya sun nuna azamar fita runfunan zabe gobe Asabar domin kammala zabubukan da ba'a kammala ba a wadansu jihohin kasar.
Bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da zama abin damuwa tsakanin ‘yan Najeriya, wani abu da ke kara daga hankalin jama'a shi ne yadda ‘yan bindiga ke kashe wadanda suka yi garkuwa da su bayan kuma sun karbi kudin fansa.
Mazauna wasu yankuna a jihar Sokoto da ke Najeriya na zaman zullumi saboda tunanin fuskantar harin ramuwa daga abokan gaba, wannan na zuwa ne biyo bayan wata arangama tsakanin fulani da hausawa a yankunan karamar hukumar Gwadabawa har rayuka suka salwanta, ciki har da jami'in Soja.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace tana ci gaba da farautar wasu da take tuhuma da hannu ga aikata laifukan da ke da alaka da tarwatsa zaman lafiyar al'umma da sunan murna akan samun nasarar zabe.
Yayin da al'ummar Musulmi a wasu kasashen duniya ke dakon soma azumi, a Najeriya ma yau ne ake soma dubin watan na Ramadan.
Yayin da hukumar zabe ta Najeriya INEC ke shirin gudanar da zabukan cike gurbi na ‘yan majalisar wakilai da na dattawa a wasu jihohin kasar, wasu masu zabe sun nuna damuwa kan matsalolin da suka yi sanadin ayyana zabukan a zaman wadanda basu kammala ba.
Duk da fadakarwa da magabata suka yi wa ‘yan siyasa a Najeriya har yanzu ana samun munanan kalamai da ke iya tunzura jama'a da tayar da fitina a lokutan zabubbuka.
Yayin da a Nigeria ya rage kasa da mako daya ‘yan kasar su sake bayyana runfunan zabe domin zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin Jihohi, Jami'an tsaro sun ce sun gano wasu shirye shiryen da manyan jam'iyyu masu adawa da juna ke yi domin tayar da fitina a lokacin zaben a wasu Jihohi.
Duk da yake tuni an kaddamar da wasu ‘yan takara da suka sami galaba a zabukan da aka gudanar ranar Assabar a Najeriya.
Yayin da a Najeriya wasu ‘yan kasar ke murna an samu nasarar zaben shugaban kasa wanda a cikin kudurin sa akwai batun magance shiga yajin aikin malaman Jami'o'i, sai ga shi wasu malaman na jami'a na shirin sanya kafar wando daya da gwamnati.
Yayin da ‘yan Najeriya suka zaku don jin sakamakon zabubukan da suka yi, wani abu da ke daukar hankali shine yadda ake samun soke sakamakon wasu runfuna abin da ke sa ba a iya ayyana dan takarar da ke da galaba amazabun.
A Najeriya wasu masu jefa kuri'a sun nuna gamsuwa da tsarin muhawara tsakanin ‘yan takarar mukaman siyasa, domin a cewarsu hakan zai ba su damar tantance wadanda ke da kudurin yi wa jama'a aiki idan aka zabe su.
Bisa ga yadda jama'a suka shiga damuwa a Najeriya saboda sauyin kudi da babban bankin kasar ya yi wanda ya kawo karancin kudi a hannun jama'a, wasu sun soma tsarin bani gishiri in baka manda, yayin da wasu suka karkafafa amfani da kudin kasashen ketare.
Yayin da 'yan bindiga ke ci gaba da aika aikarsu a fadin Najeriya, mafarauta sun ce majalisar ta ba su ikon fafatawa da miyagun su ka ikon Allah.
Yayin da ya rage saura mako uku a soma zabubuka a Najeriya masu saka ido kan zabe daga kasashen ketare na ci gaba da kwarara cikin kasar domin ganin yadda abubuwa masu nasaba da zaben ke gudana.
Domin Kari