SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da malaman Jami’ar Kimiyya da Fasahar Kere-kere ta Jihar Kebbi ke yi wa gwamnatin Jihar barazana akan rashin cika musu alkawuran da aka yi, abinda suka ce yana barazana ga ci gaban ilimi a Jami'ar da Jiha da ma kasa baki daya.
Batun yajin aikin malaman Jami'o'in gwamanati a Najeriya batu ne da ya damu wasu iyaye, dalibai har ma da ilahirin Jama'ar kasar.
Damuwa da illolin da yajin aikin kan kawo a kasar baya rasa nasaba da dalilin da ya sa wadanda suka nemi shugaban Najeriya ke saka batun magance yajin aikin malaman Jami'o'i a yekuwar da suka gudanar kafin zabe.
Kamar misali zababben shugaba kasa mai jiran gado yanzu Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya sha furta wannnan kalami a yekuwar da ya gudanar.
Bola Tinubu ne ke cewa batun yajin aikin malaman jami'o'i, shekaru hudu kacal dalibi zai kare karatu ba karin wata ko wasu shekaru saboda yajin aiki ba.
Yayin da jama'a ke fatar ganin hakan ta tabbata sai ga kungiyar malaman Jami'ar Kimiya da Fasahar Kere-kere ta Jihar Kebbi suna tauna tsakuwa kan batun alkawuran da suka ce gwamnati ta yi biris da su.
Duba da yanayin da ake ciki yanzu musamman a Jihar ta Kebbi inda sakamakon zabubukan da aka gudanar suka zowa wasu da mamaki, kamar dai yadda tsohon gwamna ya kayar da gwamna mai ci yanzu a kujerar majalisar dattawa ta Kebbi ta tsakiya, ya sa Muryar Amurka ta yi tambayi wa shugaban kungiyar ko wannan barazana da suke yi tana da alaka da batun siyasar ko faduwa a zaben.
Kokarin ji daga jami'an gwamnatin Jihar ya ci tura sai dai a lokuta daban-daban gwamnatin Jihar tana tsokaci akan hidimar da take yi wajen rayawa da habbaka darajar ilimi a Jihar.
Dangane da irin koma baya da yajin aikin malaman Jami'o'i ya kawowa sha'anin ilimi a Najeriya ya sa wasu ‘yan kasa na ganin lokaci ya yi da ya kamata malaman Jami'o'i su samu wata hanya ta sasanta matsalar ta da gwamnati maimakon dukufa ga shiga yajin aiki.
Yanzu da yake Najeriya ta samu sabon shugaban kasa da ke jiran karbar rantsuwa don soma jan ragamar lamuran kasar, fatar jama'a ba ta wuce ganin an fitar da kasar daga matsalolin da suka yi mata tarnaki ba.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir: