SOKOTO, NIGERIA - Hukumar zabe ta INEC ce ta ayyana ranar asabar 15 ga Aprilu domin kammala zabubukan da aka gudanar a watan Fabrairu da Maris da suka gabata a wasu jihohin Najeriya.
To sai dai hukumar zaben ta ce har yanzu tana bitar koken da take karba daga ‘yan siyasa kan abinda ya shafi runfunan da za'a gudanar da zabubukan, da yake wasu ‘yan siyasar sunsha kokawa akan wasu runfuna da suke korafin an saka ko an cire daga zabubukan.
Kwamishinan tarayya na hukumar zabe wanda aka tura Sakkwato don kula da ofishin hukumar a jihar, Manjo Janar Modibbo Alkali mai ritaya ya ce hukumar ta shirya kuma zata fitar da tsarin sunayen runfunan da zaben zai gudana kafin ranar da za'a yi zaben.
Ita kuwa rundunar 'yan sanda ta fitar da wani bayani dauke da sa hannun kakakinta a Sakkwato DSP Sanusi Abubakar inda take yi wa jama'a kashedi daga saba dokokin zabe cikin har da hana zirga-zirga a lokutan zaben. Hukumar zaben ta ce tana aiki tare da jami'an tsaro kuma ita ma tayi kashedi ga jama'a akan bin dokokin zaben.
Jihar Sakkwato dake Arewa maso yammacin Najeriya ta kasance jiha daya kacal da za'a gudanar da zabukan a dukan mazabun ‘yan majalisar wakilai goma sha daya da na ‘yan majalisar dattawa uku, yayinda jihar Kebbi ita ma a arewa maso yamma za'a kammala zaben gwamna da na ‘dan Majalisar Dattawa daya da na ‘yan Majalisar Wakilai biyu.
Yanzu dai zabubukan na gobe sune ake fatar zasu kawo karshen kammala zabukan da aka shata gudanarwa a wannan shekara ta 2023.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir: