A wani al'amari mai kama da nuna isa da tsabar rashin tsoron hukuma, 'yan bindiga sun fara sa haraji a wasu kyauyukan Sakkwato.
A Najeriya al'ummomin da ke fama da rashin tsaro sun fara kulla kawance domin kare jihohinsu daga barazanar ‘yan ta'adda.
Wata mata a Sokoto ta koka tare da neman a bi wa ‘yarta hakinta akan fyade da ta ce wasu mutane bakwai suka yi wa ‘yarta, kuma yanzu suna fuskantar barazana da kyama a unguwar da suke zaune.
Gwamnatin jihar Sokoto tare da hadin gwiwar kungiyar tsofaffin daliban cibiyar nazarin dubarun shugabanci dake garin Kuru Jos sun tattaunawa don samar da mafita ga matsalar tsaro.
Har yanzu ana ci gaba da fuskantar babban kalubale a fannin tsaro a jihar Sakoto saboda yadda ‘yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a wasu yankunan jihar, ko a karshen makon da ya gabata sun kai hare-hare a yankunan kananan hukumomin shagari da Tangaza.
Gwamnatin Najeriya tace tana daukar matakaI na biyan bukatun da masu zanga zangar END SARS suka bayar amma za ta gudanarda bincike duk Wadanda aka samu da hannu ga sauya akalar zanga zangar zuwa ayukkan ta'addanci zasu fuskanci hukumci.