Ministan lamurran ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya sanar da haka a wata ganawa da manema labarai a Sakkwato.
A dayan bangare kuma Kungiyar mabiya akidar Shi'a a Najeriya ta yi wa gwamnati hannuka mai sanda akan ta yi adalci wurin gyara barnar da masu zanga zangar END SARS suka yi, domin suma an yi musu makamanciyar haka.
Gwamnati Najeriya tuni da ta dauki matakan biyan bukatun masu zanga zangar inda ta fara da rushe rundunar SARS, yanzu kuma ta bayar da umurnin kwafa kwamitoci a jihohi na binciken duk mai cin zarafin talakan Najeriya domin a hukumta duk wadanda aka samu da hannu a ciki, za'a kuma fito da tsarin tallafawa iyalan wadanda aka Muzgunawa ko suka rasa rayukan su.
Gwamnatin dai ta bakin ministan lamurran ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ta yi amannar cewa matasan da suka fito zanga zangar janye yan sandan SARS sun fara ta ne da kyakkyawar manufa amma daga baya wasu bara-gurbi suka shiga suka karkata ta zuwa ayukkan ta'addanci.
Wani abu da ya dauki hankalin ‘yan Najeriya shine fasa wuraren ajiyar abinci da za'a rabawa jama'a na rage radadin da cutar korona ta haifar ana kuma wawushe abincin.
Da yake bayana rushe rundunar SARS da kafa wata runduna da zata maye gurbin ta da SWAT wadda yanzu haka jami'an ta suna karbar horo, kuma ga ayukkan ta'addanci suna wakana a sassan Najeriya domin ko a makon da ya gabata anyi wa mutane fiye da 20 yankan rago a jihar Zamfara, yaushe ne wannan sabuwar rundunar zata soma aiki? Ministan ‘yan sandan ya ce za a kamala horar dasu nan bada dadewa ba.
A wani bangaren kuma kungiyar mabiya akidar Shi'a ta Najeriya ta bakin jagoranta a Sakkwato Sidi Maniru Mainasara ta yiwa yan Najeriya jajen hasarar rayuka da dukiyoyin da aka samu a lokacin zanga zangar da aka yi, kuma ta ja hankalin gwamnatin Najeriya akan tayi adalci wajen warware matsalolin jama'ar kasar nan.
Duk da yake kungiyar ta koka akan abinda ta Kira cin zarafi da a ke yi mata, tace kofar ta a bude take idan ana bukatar a sulhunta da ita gayyatar take ganin har yanzu ba'a taya mata ba.
Saurari rahoton Mohammad Nasir cikin sauti:
Facebook Forum