A dai-dai lokacin da al'ummar wasu yankunan jihar Sokoto ke zaman zulumi saboda rashin tabbas na samun tsaron rayukan su, mahukuntaa jihar tare da sarakuna da masana sun hada hannu don neman hanyoyin tunkarar matsalar da ta waiwayi jihar.
Al'ummomin wasu kauyuka a Sokoto suna ci gaba da zaman fargaba musamman cikin dare domin sace -sacen mutane yana son zama gobarar daji a jihar.
Ko bayan hare hare da aka kai a wasu kauyuka a wannan mako ‘yan bindigar sun sake kai farmaki a Sanyinna, inda suka sace matar wani mutum da mahaifinsa.
Duk a cikin mako daya ‘yan bindiga sun kai samame a gidan tsohon Dan Majalisar tarayya Saidu Gumburawa, kuma suka yi awon gaba dashi.
Wadannan matsalolin da makamantansu ne ya karkato da hankulan mahukunta dukufa ga lalabo matakan shawo kan matsalolin.
Taron Wanda ya samu halartar mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da shugabannin hukumomin tsaro da na kananan hukumomi da tsofaffin kungiyar nazarin dubarun shugabanci da ke Jos yana da zummar tattaunawa akan kalubalayyen rashin tsaro da Nemo mafita.
Tsohon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Dahiru Abubakar shine shugaban kungiyar ta tsofaffin dalibai ya halarci taron.
A lokacin taron masana sun tattauna domin ganin an samo maslaha ga matsalolin rashin tsaro a Sokoto da makwabtan jihohi, sai dai sau da yawa ake irin wadannan tarukkan amma a karshe a kasa aiwatar da shawarwarin da aka yi matsaya akan su, kuma ga matsalolin na rashin tsaro sai ci gaba sukeyi musamman a yankin arewacin Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.
Facebook Forum