Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ke kara samarda sansanonin soji a wuraren da ke fama da matsalolin.
Matsalar rashin tsaro ta jima tana haddabar jama'a musamman a yankunan arewacin Najeriya kuma kawo yanzu dai kokarin da ake yi ya kasa magance matsalolin.
Wani abu da jama'a ke yawan kokawa akai shine karancin jami'an tsaro a yankunan su musamman da ke da matsalolin tsaro a yankunan karkara.
Yanzu rundunar sojin Najeriya ta daura damarar samar da sababin sansanonin soji domin kara yawan jami'an soji kusa da yankunan.
Wani batu da jama'a ke tsokaci dangane da matakan da mahukunta ke dauka shine yin tsambare, a dauki mataki wani wuri a bar wani, abinda ke sa wadanda ake fada da su su gudu zuwa wuraren da ba'a dauki mataki ba.
Wadansu mutanen da Muryar Amurka ta zanta da su, da ke zaune a gabashin Sakkwato inda aka aza tubalin ginin sabuwar barikin soji sun bayyana gamsuwa da wannan matakin da su ka ce zai yi tasiri idan jami'an tsaron za su kai dauki kan lokaci idan bukata ta tashi.
A nashi tsokacin, masana harkar tsaro Auwal Bala Durumin iya shugaban sashen nazarin aikata laifuka da tsaro a jami'ar Yusuf maitama Sule dake kano ya bayyana cewa, duk da ya ke wannan zai taimaka a yunkurin shawo kan matsalar tsaro, ba zai kai ga cimma gurin da ake bukata ba.
Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti: