Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Amurka jiya Lahadi don ziyarar kwanaki biyu, inda zai gana da shugaba Donald Trump akan batutuwa da dama. ‘Yan Najeriya dai sun yi kasake su ga abinda wannan ziyarar zata haifar, ita ko jam’iyyar adawa ta PDP cewa ta yi ziyarar ba zata haifar da Da mai ido ba.
Shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus, a ta bakin hadiminsa a fannin yada Labarai, Shehu Yusuf Kura, yace shugaba Buhari ya riga ya warware ziyarar kafin ma ya fara ta a wurin jama’a dayawa. Saboda ya bada wata sanarwa a hukumance yana sukar lamirin tsohon shugaba Barack Obama.
“Bayan haka a cewar Shehu Kura, kamata yayi shugaba Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya makasudin ziyararsa zuwa Amurka, shi ya sa jam’iyyar PDP ke kallon wannan ziyarar a matsayin ta kwalliya da kashe kudi.”
Tsohon shugaba Barack Obama ya amince da saida jiragen saman yaki ga Najeriya don yaki da ‘yan ta’adda a lokacin gwamnatinsa, ya kuma yaba da irin kokarin da shugaba Buhari ke yi, amma wannan bai hana shugaba Buhari sukar sa ba. Kuma saboda sakaci irin na gwamnatin shugaba Buhari ba a biya kudaden jiragentun wancan lokacin sai yanzu ne ake kokarin yin haka. A cewar Shehu Kura.
Trump ya fadi maganganu marasa dadi game da Najeriya da kasashen Afrika saboda ba ya ra’ayinsu. Shugaban ya kuma gayyaci mutane dayawa Amurka amma basu je ba, ya kuma so ya je wasu kasashen amma aka hana shi. Shehu Kura ya kara da a jingine batun adawa gefe, idan ziyarar zata amafani talaka jam’iyyar PDP zata goyi bayanta.
Za ku ji karin bayani a cikin wannan rahotn na Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum