Wata sanarwa dauke da sa hannun wani hadimin Osinbajo, Laolu Akande ya fitar, ta musanta cewa mataimakin shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara kamar yadda wata kungiya ke ikirari.
“Ana neman Ayuba Wabba da wasu shugabannin kungiyar kwadago ta kasa saboda zagon kasa da suke yi wa tattalin arzikin jihar da kuma kassara ayyukan wasu ababen more rayuwa.”
Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar, Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.
“Abin da ake bukata cikin gaggawa shi ne tsagaita wuta, sai kuma samar da daidaito da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.”
Taron, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai jagoranta, har ila yau zai duba yadda za a saukakawa kasashen nahiyar basukan da ake bin su.
Rwanda na rukuni daya ne da Madagascar, Najeriya da Tunisia. Yanzu ita ce ke gaba a saman teburin rukuninsu na A.
A ranar 10 ga watan Mayu, Janar Deby, dan shekara 37, ya kai ziyara Nijar, wacce ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasar waje tun bayan da ya gaji mahaifinsa.
Sai dai shugaban ‘yan sandan, ya yi garagdi ga jami’ansa, da su yi aiki bisa kwarewa tare da nuna tausayi da tsari da kuma kare hakkin bil adama yayin gudanar da ayyukan nasu.
A ranar Talata Majalisar da ke kula da al’amuran addinin Islama a Najeriya ta NSCIA, wacce ke karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Saa’d Abubakar, ta ayyana cewa za a yi Sallah ne a ranar Alhamis 13 ga watan Mayun 2021.
Kamfanin Dangote na da kashi 60.6 wanda mallakar Aliko Dangote ne, mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka. Sai Lafarge da ke da kashi 21.8 yayin da BUA ke da kashi 17.6
Manchester City ta zama zakarar gasar Premier, bayan da abokiyar hamayyarta Manchester United ta sha kaye a hannun Leicester City da ci 2-1 a ranar Talata.
“Rundunar sojin Najeriya na nuna takaicinta bisa wannan abin alhini da ya faru, tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan mamacin.”
Sai dai ya ce mai yiwuwa, zai koma wata kungiyar idan har ya samu tayin da ya kwanta masa a rai.
"Gidan shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Farfesa Ibrahim Gambari, na kusa da fadar shugaban Najeriya"
Shirin Duniyar Amurka na wannan mako, ya maida hankali ne kan kai ruwa rana da ake yi dangane da yunkurin da Amurka ke yi na komawa cikin yarjejeniyar shirin nukiliyan Iran wacce tsohon shugaba Donald Trump ya fice a cikinta.
“Wadanda ake zargin sun hada da, Queen Nvene, Collins Ozoemena, Samson Peter, Chika Nvene da kuma Habila Musa.” In ji hukumar ta NDLEA.
A ranar Asabar PSG ta sanar da sabunta kwantiragin, inda ta wallafa wani bidiyonsa yana sanye da wata rigar kwallo da aka rubuta 2025 a baya.
Gwaje-gwajen na awo da hukumar ta yi, sun nuna cewa nauyin hodar ta iblis ya kai gram 781.2.
“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalanta, abokanai, Majalisar Dokoki Najeriya da gwamnati da al’umar jihar Taraba.”
Domin Kari