Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nesanta kansa da wani kamfe da wata kungiya ta fara a kafafen sada zumunta, inda take nuna cewa ya ayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Wata sanarwa da kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito, dauke da sa hannun wani hadimin Osinbajo, Laolu Akande, ta musanta cewa mataimakin shugaban kasar ya bayyana aniyarsa “cikin sirri.”
“Farfesa Osinbajo bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba, amma hankalinsa na kan yadda zai dukufa wajen yin aiki a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa ne don magance matsalolin da ke fuskantar Najeriya, wadanda suka hada da neman maslaha ga matsalar tsaron kasar.” Akande ya ce.
Karin bayani akan: Osinbajo, PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A ‘yan shekarun da suka gabata, kafafen yada labarai sun ruwaito Osinbajo yana cewa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga kudu maso yammacin Najeriya ne, idan ya kammala wa’adinsa na biyu, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce musamman daga bangaren babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
A lokacin, wasu da dama sun yi hangen cewa, mataimakin shugaban kasar, yana yi wa kansa sharer fagge ne.
Sai dai a wannan sanarwa da Akande ya fitar, ta nuna cewa Osinbajo, bai sa batun neman kujerar shugaban kasar a kansa ba.
“Saboda haka, muna kira ga jama’a da su daina wadannan sake-sake, yayin da muke fuskantar kalubale da ke gabanmu a matsayinmu na ‘yan Najeriya.”