Tsohuwar ministar wacce ake wa lakabi da “Mama Taraba” ta rasu ne a wani asibiti a birnin Alkahira na kasar Masar a cewar Ango.
A duk lokacin da za a yi maganar tabarbarewar tsaro a Najeriya, musanman a arewacin kasar a wannan lokaci, mayuwaci ne a kammala zancen ba tare da an yi maganar al’ummar Fulani ba.
Annobar coronavirus ta sa an dage wasanni kwallon kafa da dama a duniya a lokacin da ta barke. Kuma har yanzu, ana buga wasannin ne ba tare da 'yan kallo ba.
“Gwamnati ta sha biyan kudin fansa. Ba wannan gwamnati mai ci kadai ba, har a zamanin mulkin Jonathan ma sun biya kudin fansa, amma suna musantawa.”
Sakamakon wannan wasa bayan doke Madrid da ci 2-0, na nufin ‘yan wasan Thomas Tuchel za su kara da Manchester City a Istanbul a wasan karshe na gasar ta Champions League.
Rahotanni sun ce an saki daliban ne a yankin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, wacce ke arewa maso yammacin Najeriya da misalin karfe hudu na yammacin Laraba.
“Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar sojoji da jami’an tattara bayanan sirri, na aiki don tallafawa gwamnatin Kaduna, da zimmar ganin an kawo karshen wannan lamari, ba tare da an sake asarar wani rai ba.”
Cikin sanarwar, kakakin Shugaban ya zargi wasu mutane “da kokarin amfani da karfi da tsarin da ba na dimokradiyya ba wajen sauya shugabanci,” a Najeriya.
Nada Mourinho na zuwa ne makonni biyu bayan da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da ke Ingila ta sallame shi.
"Mun zo ne don mu roki gwamnatin su taimaka su kubutar mana da 'ya'yanmu, ai ko dabbarka ce ta bata za ka shiga damuwa, ballantana yaronka da ka haife su."
Rahotanni sun ce da yammacin ranar Lahadi ‘yan bindigar suka kira sakataren karamar hukumar ta Yagba da kuma wani daga cikin iyalan Kolawole suka gabatar da bukatarsu.
Galabar da Atalanta ta samu, ita ta tabbatarwa da Inter nasararta, abin da ya kawo karshen mallake kofin gasar da Juventus ta yi na wani tsawon lokaci tana lashe kofin.
Bayanai sun yi nuni da cewa, Jaafar ya ce ba zai koma Najeriya ba har sai gwamnati ta bada tabbacin za ta kare lafiyarsa tare da tabbatar da walwalar aikin jarida.
Najeriya ta dauki wannan mataki ne saboda yadda cutar coronavirus ke kara yaduwa a wadannan kasashe.
Boren ya samo asali ne bayan da magoya bayan United suka fito don nuna adawarsu ga iyalan Glazers da suka mallaki kungiyar ta Manchester United, saboda sun goyi bayan kirkirar sabuwar gasar Super League da aka fasa.
Ummi ta kuma nuna takaicinta kan yadda mutane da dama suka yi ta "zaginta" a lokacin da al’amarin ya faru, tana mai cewa kamata ya yi, a yi mata nasiha ba a ci mata mutunci ba.
Manyan jami'an gwamnatin biyu na tafiya ne a mota guda a lokacin da 'yan bindiga suka bude musu wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Adebayo Solomon.
Wasu majiyoyi da dama sun ce mutanen sun kashe Muhammadu ne, gudun kada ya fallasa su, domin ya gane wasu daga cikinsu.
"Father Mbaka ya nemi ya ga Buhari, amma abin mamaki da ya tashi zuwa, sai ya taho da wasu ‘yan kwangila uku, ya nemi a ba shi kwangila a matsayin sakayyar goyon bayan da ya nunawa Buhari.”
Domin Kari