Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Yabi Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Ya Taya Ariwoola Murna


Atiku Abubakar (Instagram/ Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Instagram/ Atiku Abubakar)

“Shawarar da mai shari’a Tanko Muhammad ya yanke ta yin murabus daga mukaminsa na Alkalin alkalan Najeriya, abin a yaba ne.” In ji Atiku.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar, ya yabi tsohon Alkalin-alkalaN Najeriya mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad saboda murabus din da ya yi.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta, Atiku ya ce, mai shari’a ya cancanci yabo.

“Shawarar da mai shari’a Tanko Muhammad ya yanke ta yin murabus daga mukaminsa na Alkalin alkalan Najeriya, abin a yaba ne.” In ji Atiku.

A ranar Litinin Muhammad ya mika takardarsa ta ajiye mukamin inda ya ce yana fama da rashin lafiya.

Murabus din da ya yi na zuwa ne yayin da ake wata takaddama tsakaninsa da manyan alkalan kotun koln kasar, wadanda kwanakin baya suka rubuta wata wasika ta nuna rashin gamsuwarsu da yadda ba a ba su kulawa, ta yadda za su ji dadin gudanar da ayyukansu.

“Ina masa fatan Alheri, yayin da nake jinjina masa kan irin hidimar da ya yi wa kasa.” Atiku ya kara da cewa.

A ranar Litinin Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya.

“Ina yi wa sabon alkalin-alkalan Najeriya da aka rantsar, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola fatan samun nasara, tare da nuna goyon bayana wajen tabbatar da ci gaba da cin gashin kan fannin shari’a.” Atiku ya ce.

XS
SM
MD
LG