Takunkumin tattalin arzikin da kungiyar ta ECOWAS ta sanya wa Jamhuriyar ya yi sanadin dakatar da harkokin cinikayya da kasuwanci a yankin arewacin Najeriya, musamman a jihohi 7 da ke iyaka ta kai tsaya da Jamhuriyar ta Nijar.
A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Abdullahi Liman Nabuhari daya daga cikin dinbin ‘yan kasuwa a Kano dake safarar kayayyaki tsakanin jamhuriyar Benin, Nijar zuwa sassan arewacin Najeriya yace,
“yanzu a Cotonou kayan mutanen Najeriya da suke jibge a tashar sauke kayayyaki ta can sun kai kwantena 2500, sannan wadanda suke iyakar Gaya, wato tsakanin Jamhuriyar Nijar da Benin suna jira a bude boda sun kusa kwantena 2500, baya ga wadanda ke kan hanya suna tahowa”
Tuni dai masana harkokin siyasar kasa da kasa da sha’anin diflomasiya ke cewa, Najeriya na neman shiga sharo ba shanu game da wannan al’amari na sauyin Mulki a Nijar, domin kuwa dokokinta ba su lamunce da hakan ba.
Da yake tsokaci dangane da lamarin, Dr Mansur Datti masanin kimiyyar siyasa da harkokin huldar kasashen duniya ya ce "kudire-kudiren hulda da kasashen ketare na Najeriya ba su lamunci Najeriya ta shiga yaki da kasashen duniya ba, sai dai zata iya shiga yakin wanzar da zaman lafiya, idan kasashen suka samu kan su a cikin rikici.”
Gabanin matsalar takunmin tattalin arziki akan Nijar, Janye tallafin albarkatun mai da gwamnatin Najeriya ta yi da tashin farashin Dala sune suka fara jefa tattalin arzikin arewa dama kasa baki daya cikin wani mawuyacin yanayi a cewar Dr Lawan Habib Yahaya masanin tattalin arziki da hada hadar kudade. Yace “Wadannan abubuwa sune suka sanya matsalar tattalin arzikin arewa dana mutanen arewa ta kara ta’azzara, talauci yana ninkuwa, abinci yana kara yin karanci”
Lamarin ya sa ‘yan kasuwar suka dukufa wajen rokon hukumomin Nijar da Najeriya da-ma shugabancin kungiyar ECOWAS, su kara sassautawa, su sansanta da juna.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna