Al’amarin ya biyo bayan samun Malamin da wani jariri ne a hannu, yayin da ‘yan sintiri ke kewayawa a yankin, wanda hakan ya sa wasu shakkarsa har su ka shiga dukarsa, wanda daga bisani ya mutu.
Bayan kwashe watanni da gurfanar da Abdulmalik Tanko da sauran mutane 3 a gaban babbar kotun Kano a watan Fabareru, bisa tuhumar garkuwa da kuma kisan wata dalibar makarantarsa mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara 6, a yau Alhamis kotun ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kamar a sauran jihohi, a kano, yau kungiyar NLC ta jagoranci wata zanga zangar lumana wadda ta kunshi mambobinta don nuna goyon baya ga kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.
Shirin 'Yan Kasa Da Hukumar wannan makon zai tabo batun aikin gina babban Asibiti a garin Mayo Belwa na jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya.
Batun ciyo bashin kimanin naira biliyan guda da gwamnatin jihar Katsina tayi wadda take gudanar da aikin gina gadojin sama dana kasa a birni da kewayen Katsina na ci gaba da fuskantar caccaka daga ‘yan hamayya.
Masari yace yana nan akan bakan sa na cewa lallai al'umar jihar su tashi tsaye domin kare kan su daga farmakin 'yan ta'adda.
Yayin da masu sana’ar tuka babura masu kafa 3 da aka fi sani da A daidaita sahu a Kano da fasinjoji ke mayar da martani game da matakin gwamnatin jihar na takaita zirga zirgar baburan daga karfe shida na safe zuwa karfe goma na dare, gwamnatin ta yi karin haske dangane da wuraren da dokar ta shafa.
Yayin da 'yan sa'o'i su ka rage wa'adin da aka kara ma Kano ya cika, har yanzu maniyyata aikin Hajji na Kano fiye da rabi na zaman jira.
Yayin da hukumomin Saudiyya suka kara wa Najeriya kwana biyu domin ta sami sukunin jigilar alhazanta zuwa kasa mai tsarki, har yanzu maniyyata aikin hajji daga kasar musamman jihar Kano na bayyana shakku akan yuwuwar kwashesu zuwa Saudiyya la’akari da yadda jigilar ke tafiyar hawainiya.
Alhazan jihar Kano da suka biya aikin hajjin bana ta hanyar asusun adashen gata suna zargin hukumar alhazai ta jihar da rashin cika alkawarin cewa sune rukunin farko da za’a baiwa fifiko a yayin raba kujerun aikin hajjin bana.
Kimanin dalibai dubu 15 daga makarantun gwamnatin jihar Kano ba sa cikin jerin daliban dake rubuta jarabawar NECO da aka fara yau saboda takaddamar kudi tsakanin gwamnatin jihar da hukumar ta NECO.
Yan Najeriya, musamman manoma da mamallaka kamfanoni da masana’antu na ci gaba da bayyana damuwa akan hauhawar farashin man dizal, da ke haifar da tsadar safarar kayayyaki zuwa bangarori daban daban na kasar.
Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya tace hauhawar farashin kayayyaki da tsadar aikace-aikace da ake fama da su a kasar na tilastawa wasu daga cikin ‘yayanta rufewa kamfanonin su.
Kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Azman Air ya mayar da martani ga yunkurin gwamnatin jihar Kano na kin amincewa da kamfanin domin jigilar alhazan jihar kamar yadda hukumar kula ayyukan hajji ta Najeriya ta sahhale.
Domin Kari