Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Kisan Hanifa Abubakar


Wani mutum da aka yankewa hukumcin rataya a birnin Qazvin, Iran, 26 ga Mayu, 2011.
Wani mutum da aka yankewa hukumcin rataya a birnin Qazvin, Iran, 26 ga Mayu, 2011.

Bayan kwashe watanni da gurfanar da Abdulmalik Tanko da sauran mutane 3 a gaban babbar kotun Kano a watan Fabareru, bisa tuhumar garkuwa da kuma kisan wata dalibar makarantarsa mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara 6, a yau Alhamis kotun ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ta hanyar rataya.

KANO, NIGERIA - A zaman kotun na ranar Alhamis 28 ga watan Yuli, a karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’Abba, yace kotun ta gamsu da hujjoji guda 14 da shaidu 8 suka gabatar a yayin shari’ar, a don haka ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Abdulmalik Tanko bisa laifin da aka tabbatar a kansa na garkuwa da Hanifa da kuma yanke hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar bisa laifin daya tabbata akan sa na yin hadin baki domin garkuwa da Hanifa da nufin karbar kudin fansa, al’amarin daya kai ga hallaka rayuwarta.

Kazalika, kotun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Hashimu Isyaku mutumin da ya taimaka aka binne gawar Hanifa Abubakar bayan Abdulmalik Tanko ya sace da kuma bata shinkafar bera ta mutu. Haka kuma kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru 2 akan shi Hashimu saboda laifin yunkurin gudanar da garkuwa da karamar yarinyar da kuma wasu shekaru guda 2 bisa laifin hadin baki wajen aikata wadannan miyagun laifuka akan Hanifa.

A hannu guda kuma, Fatima Musa da a baya aka bada rahotan cewa, mata ce ga Abdulmalik Tanko, amma daga bisani ta tabbata cewa farkar sa ce, kotu ta sallame ta bisa zargin bada gudunmowa wajen aikata abubuwan da suka kai ga hallaka Hanifa Abubakar saboda rashin kwararan hujjoji akan haka. Amma kotun ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 2 a gidan gyaran hali, saboda laifin daya tabbata akanta na hannu a yunkurin garkuwa da Hanifa.

Mai shari’a Usman Na’Abba yace bayan nazari mai zurfi akan dukkanin hujjojin shaidun da lauyoyin masu gabatar da kara suka gabatar, kotun ta gamsu dasu, a don haka ta yi amfani da su wajen tabbatar da adalci ga masu kara da wadanda aka gurfanar gabanta.

Gabanin bayyana hukuncin kotun, lauyar Abdulmalik Tanko da mutanen biyu, Barrister Hasiya Muhammad Imam ta roki kotun ta yi adalci akan wadanda ake tuhuma, musamman shi Abdulmalik, la’akari da cewa, magidanci ne da ‘yaya.

Shi kuwa lauyan gwamnati da ke kare marigayiya Hanifa Abubakar, Barrister Musa Abdullahi Lawan, ya roki kotun ta tabbatar da adalci ga iyayen Hanifa, musamman mahaifiyar ta. Ya kuma roki kotun ta yi hukunci mai zafi akan su Abdulmalik Tanko.

Yanzu haka dai Abdulmalik Tanko, da Hashimu Isyaku, da kuma Fatima Musa, na da kwanaki 30 su daukaka kara muddin ba su gamsu da hukuncin babbar kotun ta Kano ba, kamar yadda dokar kasa ta ba su dama.

Kazalika, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne zai sanya hannu gabanin zartar da wannan hukunci bayan karewar wa’adin da doka ta bai wa wadanda aka yanke wa hukuncin ba tare da sun daukaka kara ba.

XS
SM
MD
LG