Rundunar yan sanda a Kano ta ce ta kama 6 daga cikin Jami’an rundunar tsaro ta Vigilante da ake zargi da hannu wajen mutuwar wani malamin makaranatar allo mai suna Mallam Musa Lawan mazaunin unguwar Dabai ta yankin karamar hukumar Dala a birni da kewayen Kano. Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Malamai a Kanon suka yi tir da yanayin daukar doka a hannu game da lamarin.
Al’amarin ya biyo bayan samun Malamin da wani jariri ne a hannun, yayin da ‘yan sintiri ke zagaye a yankin, da hakan ke nuna shakku da alamomin tambaya akan malamin.
Jami’an tsaron na vigilante sun yi zargin cewa, alaramma Musa Lawan sato jaririn ya yi, la’akari da yanayin da dare da cewa, shi na miji ne ba mace ba, kuma babu wata mace a tare da shi a wannan lokaci.
Sai dai a nasu banagren, almajirai da abokan malamin dai sun yi zargin cewa, ‘yan sintirin sun dauki doka a hannunsu ta hanyar lakada masa duka har rai ya yi halinsa.
A cewar wani abokin mallamin, mai suna Malam Mohammed Salisu, gabanin amininin nasa marigayi Malam Musa Lawan ya sanar da su jami’an tsaron hakikanin al’amari, sai kawai ‘yan sinitirin suka yi burus suka ci gaba da afka masa, har ya fita daga hayyacinsa.
Shi kuwa Muhammad Auwalu Salisu dan Uwa ga Malam Musa Lawan ya je ya tarar da Malamin a ofishin ‘yan sintirin cikin mummunan yanayi gabanin rasuwar sa, yana mai cewa ba za su amince da kisar gillar da aka yi wa dan uwan nasu ba, lallai tilas ne hukuma ta kwato musu hakki, kuma wajibi ne a gurfanar da wadannan ‘yan Vigilante a gaban kuliya a yi musu hukunci dai-dai da abin da suka aikata.
Ita kuwa kungiyar Mahaddata alkur’ani ta Najeirya ta yi Allah wadai da wannan kisa da aka yi wa malam Musa, sai dai ta yi kira ga almajiran malamin da su kiyaye doka, tare da bari jami’an tsaro su yi aikinsu, a cewar shugaban kungiyar na kasa Gwani Lawi Gwani Danzarga.
DSP Abdullahi Kiyawa shine kakakin ‘yan Sanda a Kano ya ce ya zuwa yanzu sun kama mutane 6 daga cikin Jami’an tsaron na Vigilante da ake tuhuma da hannu wajen wannan gisar gilla ga Malamin Makarantar allon, yana mai cewa, Jami’an rundunar sun ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiyar al’amari.
Yayin da al’uma ke dakon sakamakon binciken ‘yan sandan dangane da wannan batu, hakan na nuna bukatar karin kiyaye doka da oda hatta a tsakanin Jami’an tsaro dake rike da amanar kare lafiya da dukiyar al’uma.
Saurari cikakken rahoton daga Mahmud Ibrahim kwari: