Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da bullar cutar Mashako (Diphtheria) a jihohi hudu na fadin kasar.
A cikin shirin na wannan makon mun yi magana ne akan cututtukan da suka shafi cikin ciki da hanjin ‘dan adam.
Har yanzu dai cutar kwalera dake sa amai da gudawa na cigaba da addabar mutane a Najeriya.
A cikin shirin na wannan makon mun yi magana ne akan tsarin iyali domin bada tazarar haihuwa, mai kula da marasa lafiya da kuma ungozoma.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin gwamnatin sa na karshe, yayinda ake ci gaba da fama da kalubalen tsadar rayuwa a kasar ta Afirka ta Yamma mai arzikin man fetir kuma mafi yawan bakar fata a duniya ba.
Biyo bayan ambaliyar ruwa mafi tsanani a tsawon shekaru da a ka yi fama da shi a Najeriya a damunar da ta gabata, akwai sassa da dama da har yanzu ba su samu dauki ba.
Har wannan zamani da za a ce asibitocin sha-ka-tafi na nan a kusan kowane yanki na Najeriya; amma mutane kan yi amfani da magungunan gargajiya a wasu cutuka na yau da kullum kamar gembon ciki, zazzabin cizon sauro, mayawuya da sauran su.
Biyo bayan nasarar kammala wallafa littattafai 6 na gajerun Hadisan Manzon Allah da Sheikh Muhammad Kabir bin Abdullahi Alkanawy ya rubuta, matashin malami Abubakar Musa ya fassara biyu daga litattafan don gyara tarbiyya.
Shirin ya duba alamomi, matakan kariya da ya kamata a yi la'akkari da su kan cuttukan na shawara da zazzabin Lassa tare da Dr. Maryam Ahmad Almustapha.
Kwararre a fannin kwanyoyin cuta na Virus Dr. Isa Adamu Mabo, ya yi karin haske kan yadda ake kamuwa da cutar kyandar biri, alamominta da matakan da ya kamata a dauka idan an kamu da cutar.
A lokacin da muke gab da shiga sabuwar shekara, shirin lafiya uwar jiki zai yi bitar wasu muhimman maudu'ai da muka tattauna akai.
An gudanar da taron rantsar da sabbin shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da aka zaba bayan kammala wa’adi na tsoffin shugabannin kungiyar na wa’adi biyu a tsawon shekara 8 karkashin Muhammad Kiruwa Ardon Zuru.
Sashen tattalin arziki da zamantakewa na Majalisar Dinkin duniya ya fitar da wani rahoto dake nuna cewa yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 216 a shekarar 2022, da hakan ya kai kashi 2.7 na al’ummar duniya.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa za ta fara tattaunawa da hukumar aikin hajji da umrah ta Saudiyya don fara yarjejeniyar aikin hajjin badi.
An gunadar da bukin yaki da ciwon suga da kuma ake kira ciwon sukari na Hukumar lafiya ta duniya bana da taken 'Samun ilimi game da ciwon sukari don kariya. '
Hukumar lafiya ta duniya ta ware ranar 24 ga watan Oktoba na kowacce shekara a matsayin ranar yaki don kawar da cutar shan inna a duniya.
Kungiyar masu gwanjon kayayyaki ta Najeriya tayi zargin cewa hukumar hana fasa kwauri wato kwastam na saka son zuciya da almundahana game da yadda take gudanar da ayyukan ta.
Domin Kari