Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijer HALCIA da kungiyar tallafawa kasashe masu tasowa ta kasar Jamus GIZ, sun kaddamar da wani shiri a Birnin N'Konni na yiwa jama'a takardun shige da fice na kasashen ECOWAS ko CEDEAO.
"Gaskiya muna kira ga 'yan kasuwa a cikin wannan lokaci na azumi, muna azumi ne domin neman lada, saboda haka, mu tausaya wa mutane, domin wani lokaci idan ana azumi kaya kan yi tsada." Inji Pastor Musa.
Yanzu haka ana gudanar da wani taron koyawa matasa ayyukan yi a Jamhuriyar Nijar, domin a canja tunaninsu wajen yin tafiya mai hadari da su ke yi zuwa kasashen Turai, inda su ke rasa rayukansu a cikin Sahara ko Teku.
Jihar Zamfara da ke makwabtaka da Nijar ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda a lokuta da dama sukan yi garkuwa da mutane domin neman makudan kudaden fansa.
Wasu mutane da ba a san ko su wanene bane sun kai hari a wani gari da a ke kira Rungumawar Jawo dake cikin karamar hukumar mulkin Illela ta jahar Sokoton tarayar Najeriya.
Kungiyar Ahmadiyya wacce ta samo asali daga kasar Pakistan, yanzu haka ta samu karbuwa a fadin Jamhuriyar Nijar, inda tayi taron ta na shekara da ake kira Jalsa Salana da aka bude shi jiya a birnin Konni.
Bukin Kirsimeti a Birnin N'Konni da irin rawar da hukumomi suka taka, na baza jami'an tsaro domin kariyar lafiya jama'a da majami'u, haka al'ummah Musulmai sun yi ma Kiristoci barka da shagulgula.
Al’ummar Musulmi a Jamhuriya Nijar sun marawa abokan zamansu Kiristoci baya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti.
Rundunar 'yan sanda jahar Sokoto tayi nasarar kama wani mutum da ya yi yinkurin tsallakowa daga kan iyaka Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya dauke da harsasai guda dari tara.
Gwamnatin wasu Jihohin Jamhuriyar Nijar a Tahoua, da Dosso tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Sokoto a Najeriya,sun gudanar da taron tsaro na gaggawa.
A wani yinkuri na neman sanin samfur din yanayin gidaje a Janhuriyar Nijar, hukumar kidaya za ta dau alkaluma a dubban gidaje a wurare wajen 250 a kasar.
A Janhuriyar Nijar mai cike da al'adu iri-irir, an nada Sarkin Dogarawan Abzin a wani kasaitaccen da ya burge masu wannan al'adar da kuma 'yan kallo.
A cigaba da yaki da safarar mutane da muggan kwayoyi da ta ke yi, Janhuriyar Nijar ta lashi takobin ganin bayan masu aikata wadannan manyan laifuka a kasar.
An kaddamar da aikin gina wani katamfaren kamfanin siminti na hadin guiwa tsakanin kamfanin Dan Gwate da kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar, da za a gina a cikin Gundumar Keita dake jahar Tahoua.
Asusun talafawa yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya , UNICEF na fadakar da 'yan jarida game da illolin aurad da yara mata da ba su kai shekaru 18 da haihuwa ba.
Yau ranar 12 ga watan Mayu ake bikin tunawa da ma’aikatan jinya a fadin duniya.
Domin Kari