Hukumomin da ke da alhakin shirya alhazai zuwa kasa mai tsarki daga Jamhuriyar Nijar na ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsaki akan aikin hajjin bana, ganin cewa wasu daga cikin maniyyatan basu ida biyan kudin aikin hajjin a bana. Ganin kuma ana daf da fara tashi daga birnin Yamai ranar 30 ga watan Yuli zuwa kasa mai tsarki.
"Har yanzu biyan kudin jirgin nan, ana nesa da abin da ya kamata a biya gaba daya," inji Alhaji Mani, magatakardan hukumar kula da aikin Hajji ta Jamhuriyar Nija.
Ya ci gaba da cewa daga cikin mutane 8867 da suka rubuta sunayensu, 3300 kadai aka samu sun biya kudaden da ake bukata daga garesu.
"Bada kudin na da muhimmanci saboda duk mai son zuwa dole ne sai an yi mashi biza, da guzuri da tikitin jirgi," inji Alhaji Mani, abubuwan da sai in an biya ne za a samar.
Kampanonin dake aikin hajji sun fara nuna damuwa kan rashin biyan kudaden jiragen da zasu yi jigilar maniyyatan.
Saurari rohoton Haruna Mamman Bako
Facebook Forum