Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kwato matsayinsa na attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
Sama da kwanaki 100 da sace daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau na jihar Zamfara, iyayen yaran sun sake kaiwa gwamnati kokensu don ta kara kaimi wajen biyan bukatun da ‘yan ta’addan suka gabatar na musayar mutanensu dake tsare a hannun gwamnati da ‘ya’yansu.
Hamshakin dan kasuwa, dan asalin kasar Afrika ta Kudu, Johann Rupert ya sha gaban attajirin dan kasuwa Aliko Dangote inda ya zama wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta fitar.
Karamin ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a wata hira da muryar Amurka a Abuja. Bello Matawalle dai ya jadada cewa, an dauki kwararan matakan kiyaye sake afkuwar irin iftila'in da ya faru a kauyen Tudun Biri dake Jihar Kaduna a Najeriya.
Kwanaki 16 cir kafin a cika wa’adin da kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPCL ya sanya na fara aikin matatar man fetur na Fatakwal, masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur sun nuna shakku ga yiyuwar hakan ganin cewa ba’a ma fara aikin gwaji a matatar da ake sake ginawa din ba.
Masu sharhi da masana harkokin hakkin dan Adam na ganin ana samun karuwar take hakkokin bil’adama a Najeriya.
‘Yan Najeriya sun fara nuna rashin jin dadinsu da salon kungiyoyi da suka ce talaka suke kara kuntatawa, kasa da sa’o’i 24 da fara yajin aikin gamagari da kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC suka fara.
Mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC da TUC sun tsayar da ayyuka a filin tashi da saukan jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja don nunawa gwamnati bacin ransu a game da zalincin da aka yiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.
Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke bai karya masa gwiwa ba a kan ganin an sami sauyi a sabuwar Najeriya.
Kotun kolin Najeriya mai alkalai 7 karkashin jagorancin mai shari’a John Nyang Okoro, ta yi watsi da kararrakin da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Leba suka daukaka kan nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar da dan takarar shugaban kasa karkashin Inuwar Jam’iyyar PDP yayi na gabatar da sabbin hujojji a gaban ta.
Kotun kolin mai mambobi bakwai da ke samun jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ne ta yanke wannan hukuncin a ranar Litinin jim kadan bayan da lauyoyin jam’iyyun da suka daukaka kara da wadanda ake kara suka amince daya-bayan daya da bayanansu.
Matsalar faduwar darajar kudin naira abu ne da ya kara ta’azzara musamman a makonnin bayan-bayan nan inda ake sayen dala daya a kan naira 995 zuwa dubu 1 da 100 kasancewar karancin dala a cikin Najeriya.
A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar kayayyakin da suka shafi makamashi kamar iskar gas, man fetur da wutar lantarki, tare da hauhawar farashin da ake samu kusan kullum, gwamnatin kasar ta ce za’a sami walwala nan ba da jimawa ba.
Domin Kari