Har yanzu dai ‘yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da yan ta’ada suka yi garkuwa da su bayan tarwatsa wani bangaren jirgin da bam na neman gwamnatin kasar ta dube su da idon rahama.
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya maida martani kan cece-ku-cen da ya biyo bayan rabawa sarakunan gargajiya a jihar motoci da kuma alakantan sayen motocin da zunzurutun kudin da aka kiyasta cewa ya kai biliyoyin nairori.
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina kuma shugaban kwamitin tantance 'yan takara da suka tsaya neman mukamai daban-daban a karkashin jam’iyyarsu ta APC da ta ke gudanar da babban taronta a yau, 26 ga watan Maris, ya bayyana cewa kwamitinsa ya sami nasarar tantance 'yan takara 189.
Wasu matasa da masana kundin tsarin mulki na ganin cewa ya dace a cire bayanin addinni da asalin jihar da mutum ya fito a takardar bayanin mai neman aiki wato CV don rage matsalolin kabilanci a kasar.
A daidai lokacin da kamfanonin jiragen saman Najeriya suka yi barazanan janye aikinsu na jigilan fasinjoji a fadin kasar sakamakon tsadan makamashin tafiyar da jiragensu nan da kwanaki biyu, kamfanin NNPC tare da hadin gwiwan mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar sun shiga tsakanin bangarorin .
Har yanzu ba’a a sami cikakken bayani kan adadin ‘yan fashin daji da aka kashe ba sai dai rahotannin sun yi nuni da cewa ba bu mutanen gari da suka rasa ransu.
El-Rufai ya kara da cewa shugaba Buhari ya umarce su da su nemi hanyar da ta dace kuma bisa ka'ida wajen sauke Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikon jam’iyyar ta APC.
A ranar Laraba hukumomin Najeriya suka kaddamar da shirin kwaso 'yan kasar da suka makale a kasashen Romania, Poland, Hungary da Slovakia da ke makwabtaka da Ukraine.
Kasa da sa’o’i 24 da Majalisun tarayyar Najeriya suka yi watsi da kudurin da ke nemawa mata kari na kaso 35 cikin 100 na muhimman mukamai musamman na siyasa a kasar, daruruwan mata a karkashin inuwar kungiyoyi da dama suka fito zanga zangar lumana domin nuna bacin ransu game da matakin Majalisun.
Jam’iyyar APC mai mulki ta dage babban taronta da ta shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Febrairu zuwa 26 ga watan Maris.
Rochas ya kara da cewa a halin da Najeriya ke ciki, al'umar kasar na bukatar shugaba mai tausayin jama’a.
A daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantan karancin man fetur a kusa fadin kasar, kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ya jadada cewa ba da gangan aka shigo da gurbataccen man fetur mai cike da sinadarin Methanol mai yawan gaske cikin kasar ba.
Likitoci dake kula da masu fama da ciwon amosanin jini da aka fi sani da ciwon sikila sun bukaci gwamnatin Najeriya ta duba lamarin masu fama da ciwon sakamakon karancin kayan aikin kula da su da kuma karancin asibitoci na musamman, da kuma karancin kawararrun likitoci.
Domin Kari