Hukumar tsaron fararen hula a Gaza ta fada cewa, wani harin da Isira’ila ta kai da sanyin safiyar ranar Asabar ya kashe mutane 15 daga wani iyalan Falasdinawa, da su ka hada da yara tara da mata uku.
Rikicin ya samo asali ne daga yunkurin kashe al-Baqra da aka yi a ranar Juma’a, wanda mayakansa suka daura alhakinsa kan al-Shahida Sabriya, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.
Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta fada a yau Asabar cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon harin sama na baya bayan nan da Isira’ila ta kai kan wata makaranta da Falasdinawa ke zaune wadanda suka rasa matsugununsu ya haura 90.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasa kai tsaye a gobe Lahadi 4 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 7 na safe agogon kasar.
Matasa a sassan Najeriya sun fara gudanar da zanga zanga kan tsadar rayuwa da sauran matsaloli da suke addabar kasar.
Dan kasar Serbia Novak Djokavic ya kafa tarihin kai wasan kwata-fainal na wasan tennis a gasar Olympics karo hudu a jere, bayan da ya doke dan kasar Jamus Dominic Koepfer da ci 7-5; 6-3 a ranar Laraba.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada sababbin Sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Karaye, Rano da kuma Gaya.
Domin Kari