Masar ta ba da tabbaci a ranar Alhamis cewa ta bullo da wani tsari da zai iya kawo karshen rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza wanda ya kunshi matakai uku da za su kai ga cimma matsayar dakatar da bude wuta, tana mai cewa yanzu tana jiran a ba ta amsa kan wannan bukata da ta mika.
Akalla mutane 40 ne suka mutu sakamakon fashewar wata tankar iskar gas a Arewa ta tsakiyar kasar Laberiya, a cewar babban jami'in kula da lafiya na kasar ta yammacin Afirka, Francis Kateh, a ranar Laraba.
A ranar Talata Majalisar Dinkin Duniya ta nada jami'ar da za ta sa ido kan jigilar kayayyakin jin kai zuwa zirin Gaza, a wani bangare na kudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince da shi a ranar Juma'ar da ta gabata don bunkasa ayukan jin kai.
Wata babbar mota dauke da kayan abinci da mutane sama da 200 ta yi hatsari a jihar Neja da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya, inda ta kashe fasinjoji 25 tare da raunata wasu da dama, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Laraba.
A ranar Talata ne akasarin ‘yan majalisar dokokin Afirka ta Kudu suka kada kuri’ar amincewa da kudirin rufe ofishin jakadancin Isra’ila tare da yanke huldar diflomasiyya har sai Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta a Gaza.
A ranar Talata Isra'ila da Hamas sun kusa cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta na wani dan lokaci a yakin da suke yi na tsawon makwanni shida a dalilin dimbin Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza da nufin yin musanya da Falasdinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.
A Jamhuriyar Nijar ma, manoma da dama na fama da kalubalen sauyin yanayi, inda wasunsu suke barin aikin gona suke komawa ga wasu harkoki kamar hakkar ma’adinai, da wasu rahoranni
Babban bankin Najeriya ya ce tsofaffin takardun kudi da ake shirin daina amfani da su a wata mai zuwa, yanzu za a ci gaba da aiki da su, hakan ya kawo karshen rashin tabbas na watanni bayan da yunkurin cire su a farkon wannan shekara ya haifar da karancin kudi.
Nijar za ta fara fitar da gangan danyen mai dubu 90 domin siyarwa a kasuwannin duniya; Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta dauki tsauraran matakan tsaro na tabbatar da zabukan da aka gudanar ranar Asabar sun kammalu lami lafiya, da wasu rahotanni
Domin Kari