Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Hutun Tunawa Da Martin Luther King Ta Ci Karo Da Bikin Rantsar Da Trump


Ranar MLK - Ranar Rantsar da Donald Trump - Janairun 20, 2025
Ranar MLK - Ranar Rantsar da Donald Trump - Janairun 20, 2025

Sa’ilin da zababben shugaban kasa Donald Trump ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka a babban dakin taro na Majalisar Dokokin Kasar ta Capitol, ya yi haka ne yana fuskantar mutum mutumin rabaran Martin Luther King a bisa tarihin hutun tunawa da King na tarayyar kasar, 20 Janairu

Wannan sabani ya haddasa damuwa a zukatan wasu masu rajin kare hakkin bil adama dake fatan cika buri marigayi rabaran king na kawowa al’umma sauyi ba tare da tashin hakali ba.

Ana rantsar da sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump
Ana rantsar da sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump

Shagulgulan bikin karrama King da kokarin yada manufarsa ta samar da al’umma mai adalci zasu gudana a fadin kasar yayin da dimbin al’ummar Amurka ke sanya idanu akan yadda ake musayar iko cikin lumana a babban birnin kasar.

Bukukuwan dake gudana a lokaci guda sun haifar da yanayi iri 2 a zukatan shugabannin kungiyoyin farar hula, wadanda a bayyanai suke sukar kalamai da matsayar Trump akan babancin jinsi da hakkokin farar hula yayin yakin neman zabensa na 3. Saidai shugabanni da dama ciki harda iyalan King, na kallon wannan gamin-gambizar hadakar bukukuwan a matsayin wani bambanci mai ban takaici kuma dama ta sake mayar da hankali akan dabbaka fafutukar kare hakkokin farar hula a wani sabon babin siyasa.

“Na ji dadi data faru a irin wannan rana saboda ta bayyanawa amurkawa dama duniya baki daya bambancin a bayyane. Wannan shine tafarkin da muke so mu bi-ko kaima shi kake ka bi?” a cewar Rabaran Bernice King, karamar ‘ya a wurin marigayi King kuma shugabar cibiyar King.

“Ba rana ce da zai iya haskakawa a matsayin tauraro ba, wanda shine burinsa,” kamar yadda diyar King ta bayyana game da Trump. “Dole ne yayi hakuri da wannan tarihi da ranar ta gadar, ba tare da la’akari da yadda ya sarrafa ko ya gabatar da jawabinsa ba, ina fatan wadanda suke kewaye da shi zasu bashi shawara ya mutunta ranar yadda ya dace a jawabinsa.”

Rev. Dr. Bernice King, Atlanta, Georgia
Rev. Dr. Bernice King, Atlanta, Georgia

Wannan shine karo na 3 a cikin kusan shekaru 40 tun bayan da ranar hutun tunawa da King ta zo daidai da ranar rantsar da shugaban kasa a dokance. An rantsar da Shugaba Bill Clinton da Barack Obama a wa’adin mulkinsu na 2 a makamanciyar wannan rana. Dukkaninsu sun yabawa King a jawabansu, abin jira a gani shine yadda Trump wanda ya taba yin ikrarin karya akan cewar yawan jama’ar da suka halarci bikin rantsar da shi na farko sun ninka wadanda suka halarcin gangamin macin da King ya tara a Washington, zai shaida wannan rana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG