Da misalin karfe 1 na safe ranar 26 ga Maris ne Larry DeSantis ya nufi aikinsa na biyu a gidan burodin Herman da ke yankin Baltimore.
Wata gobara da ta tashi a wani gidan rawa da ke birnin Istanbul a lokacin da ake yin gyare-gyare a ranar Talata, ta kashe mutane akalla 27, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Masu ibada a wani masallaci da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tsere a ranar Talata a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far wa mazauna yankin.
Wani harin da Isra’ila ta kai ya kashe ma’aikatan jin kai bakwai da ke aiki da kungiyar abinci, lamarin da ya sa kungiyar ta World Central Kitchen ta dakatar da kai kayan agaji zuwa Gaza a ranar Talata, inda hare-haren Isra’ila ya jefa dubban daruruwan Falasdinawa cikin matsananciyar yunwa
Malamin Addinin Kiristan nan na Najeriya Bishop Mathew Kuka ya caccaki tsarin yadda ake rabon kayan tallafi ga 'yan Najeriya a daidai lokacin da halin matsin rayuwa ke kara ta'azzara a kasar.
Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Talata zuwa Dakar, Senegal, domin halartar bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.
A jihar Kebbi da ke Najeriya, wani lamari ya afku inda ake zargin wani soja ya harbe wani mutum har lahira saboda sace kayan abinci. A cewar wata majiya a jihar, an tura sojoji ne domin hana sace-sacen a wani wurin da aka ce mazauna yankin na kwashe kayan abinci.
Babbar jam'iyyar adawa ta Turkiyya ta ci gaba da rike madafun ikonta a wasu muhimman biranen kasar tare da samun gagarumar nasara a wasu wurare a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.
Yadda kubutar da daliban Kuriga wanda yazo kwana guda kafin cikar wa’adin da ‘yan bindigan suka gindaya ya haifar da ce-ce-ku-ce a game da yadda aka yi a ka kubutar da su; Matsalar kwararar baki a birnin New York na Amurka ta rubanya har sau uku daga kasashen Yammacin Afirka, da wasu rahotanni
Domin Kari