Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya shiga tsaka mai wuya kan yadda zai shiga tsakani dangane da kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Joe Biden na ya janye takararsa.
Wani jirgi mara matuki kirar Iran da 'yan tawayen Houthi na Yemen suka tura a birnin Tel Aviv ranar Juma'a, ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da raunata akalla 10 a harin farko da kungiyar ta kai kan Isra'ila.
A wani samamen kasa da kasa da ya maida hankali akan kungiyoyin batagarin dake aikata laifuffuka a nahiyoyi 5 masu tushe a kasashen yammacin Afrika, ‘yan sanda sun kama mutane 300 sun kwace tsabar kudi dala miliyan 3 da toshe asusun banki 720, a cewar rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol.
Kwana na 3 na babban taron jam’iyyar Republican zai soma a daren yau Laraba karkashin jagoranci hadakar Donald Trump da JD Vance da aka zaba a baya-bayan nan zasu maida hankalinsu kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa da manufofin kasashen ketare.
Hukumomin kasar Thailand sun bayyana a yau Laraba cewar, binciken farko da aka gudanar akan musabbabin mutuwar gawa ya nuna cewar akwai burbushin sinadarin cyanide a jinin wasu ‘yan vietnam 6 da baki Amurkawa a otel din “Central Bangkok Luxury”
Ruftawar wata haramtacciyar mahakar zinariya tare da birne mahakan da ransu ya hallaka akalla mutane 5 a arewacin kasar kenya, a cewar hukumomin yankin.
Bayan shafe kwananki 20 a hannun yan bindiga, Hajiya Hauwa’u Adamu mahaifiyar mawakin Najeriya Dauda Kahutu Rarara da aka fi sani da Rarara ta samu kubuta da saduwa da ‘danta.
Shahararrun ‘yan kasuwa na duniya da ‘yan siyasa sun fara hallara babban birnin kasar India a ranar Juma’a domin halartar daurin auren karamin dan Mukesh Ambani, wanda ya fi kowa arziki a Asiya.
Domin Kari