Labaran Afirka a takaice
Bari mu fara da kasar Kenya inda shugaban yan adawa Raila Odinga yace hadakar kungiyoyinsa ba zata yi mulkin kasar ba tare da barayi, kwanaki biyu bayan da kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben saboda magudi.
A kasar Burundi masu bincike na majalisar dinkin duniya sun zargi gwamantin kasar da cin zarafin bil adama da suka hada da kisa da azabtarwa kana sun yi kira a gaggauta shigar da kara a kotun kasa da kasa na manyan laifuka.
Fire ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya caccaki cibiyoyin 'yan jaridun kasar, akan cewa suna yi masa zagon kasa akan margin cin hanci da rashawa.
Hukumomi sun ce akalla mutane 44 sun mutu a Nijar, wasu dubu 70 kuma sun rasa matsugunnan su sanadiyyar ambaliyar ruwa.
Dan Majalisar Dattawan Amurka Sanata Christopher Coons ya jagoranci wata tawaga mai mutane shida da ta hada da Jakadan Amurka a Najeriya zuwa Maiduguri domin gani da ido da yadda sojojin Najeriya ke yaki da Boko Haram tare da karfafa masu.
Saudi Arabia: an fara gudanar da aikin hajji na kwanaki biyar inda dubban jama’a zasu fara zagaya ka’aba dake Mecca, da yin addu’oi.
Senegal: Jama’a da dama a Dakar, suka yi raye raeye da kade kade bayan kotu ta saki dan gwagwarmayan nan Kemi Seba, wanda aka tsare bayan ya kona takardar kudi ta CFA, a wajan wani taro a yunkurinsa na kin amincewa da sabuwar takardar kudin.
Afghanistan: ‘Yan Sanda sun shaidawa VOA cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari wa jama’a a wajen wani bank a Kabul inda ya kashe mutane a kalla 5 tare da raunata 9 kuma Taliban ta dauki alhakin.
Benin: Gungun masu zanga-zanga a Benin, sun nemi da daina amfani da takardan kudin sefa da kuma a saki Kemi Seba da aka ake tsare da shi tun Jumu’a bayan ya kona takardar kudin sefa 5000.
Yawancin birnin Houston wanda ya kasance gari na hudu mafi girma a Amurka yana karkashin ruwa sanadiyar muguwar guguwa Harvey.
Bari mu kara lekawa a kasar Kenya inda doka mafi tsanani a duniya ta haramta anfani da leda ta fara aiki a yau ranar Litinin, inda sayar da say eke jefa mutun gidan kaso na tsawon shekaru 4 ko biya tara na dubu 40 na dalar Amurka.
LIBYA: A kalla mutane 11 aka fille wa kawuna a wani hari da ‘yan kungiyar ISIS suka dauki alhakin kaiwa a wani wurin binciken kan hanya da sojojin Libiya sukai wa lakabi da Khalifa Haftar
YEMEN: Sojojin Saudiyya sun kai hari a babban birnin Yemen, Sanaa, inda suka kashe akalla fararen hula 12, ciki har da yara.
Domin Kari