Kwamandan soji mai barin gado Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya karyata jita jita da wasu kafafan yada labaru suke yadawa, kan cewa an koresa daga wiki. Ya mika shuganabancin shiyar zuwa ga Manjo Rogers Nicolas a Maiduguri.
Hukumar kare hakkin bil adama a Najeriya ta ce za ta dauki matakan kare hakkin 'yan gudun hijira.
Labarun duniya a takaice
An gano gawarwakin dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Tanzania guda 15, da aka kashe a wani hari da ake zargin ‘yan tawayen Uganda ne suka kai a makon da ya gabata.
A Somaliya mutane fiye da 600 ne suka yi zanga zanga domin nuna rashin amincewarsu da matsayin shugaba Amurka Donald Trump na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Israila.
Ana ci gaba da yin Zanga zanga a dukanin kasashen dake da mafi yawan Musulmi a yau Juma'a, domin nuna kin amincewa da yin Allah waddai da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na Ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Israila.
‘Yan cirani daga Najeriya su fiye da 140 da suka dawo daga Libya sun nuna farin cikinsu saboda kubuta daga inda suka kwatanta da jahannama sanadiyar ukubar da suka sha a wuraren da aka tsaresu akan hanyarsu ta zuwa Turai.
A Palesdinu daruruwan yan kasar ne suka yi zanga zanga nuna kin amincewarsu akan sanarwa da shugaban Amurka Donald Trump ke shirin yi na ayyana Birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Israila a hukumance.
An fara Zaman Shara'a na shekara zuwa shekara a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar wanda ke mayar da hankali kan manya-manyan laifufukan da ka aikata. Ibrahim Harouna mataimakin shugaban kotun daukaka kara ta Yamai yayi karin bayani.
An ayyana ranar 3 ga watan Disemba ta kowace shekara Ranar Nakasassu, ranace da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da nakasassu na duniya. A Maiduguri wasu nakassasu sun bayyana muna korafe korafensu domin duniya ta sa taimaka musu.
An nuna rahoto a kan majigin nan mai suna TATTAKI DAGA BAKAR AKIDA wa hukumomi dauko daga Gwamnan jahar Maradi da mukaraban sa, da shugabanin tsaro na jahar da kungiyoyi da malamai na islama da kirista da mata da matasa a jihar Maradi
Kafar Talabijin ta gwamnatin kasar Koriya ta arewa ta nuna hoton bidiyon shugaban kasar Kim Jong Un yana kallon kaddamar da gwajin makamin Nukilya na baya bayan nan yana murna tare da kwararru kan makamin nukiliya.
Domin Kari