Adadin mutanen da suka mutu a wata fashewa da ta auku a Idlib na Syria, ya kai 19 daga 13, mutanen da mafi yawansu fararen hula ne.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsalar azabtar a gidajen yarin Libya ya yi tsamari, gidan yarin da ke hannun kungiyoyi masu dauke da makamai.
A Japan A yau litini mutane biyar suka ji raunuka bayan wata girgizar kasa da karfin ta yakai 6.1 a ma’uani, wadda ta ratsa kilomita 12 na karkashin kasa a kusa da Oda.
Jama’a da dama suka ji raunika a wata arangama tsakanin ‘yan tawaye da jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD a yankin PK5 na musulmi a Bangui.
DRC: Shugaban hukumar zaben Congo-Kinshasa, Corneille Nangaa yace ba za a fasa gudanar da zabe ba duk da cewa an gano magudi cikin wadanda suka yi rijistan zaben.
Gaza Strip: Falasdinawa da ke zanga-zanga kan iyakar Gaza da Isra’ila na kona tayoyi yayin da arrangama ya kaure, mako guda bayan da irin zanga-zangar ya kazance har dakarun suka kashe falasdinawa 19.
Kwararru sun yi zama akan mahimmancin aikin jarida a Jami'ar George Washington dake nan Amurka inda tsohon daraktan Muryar Amurka David Ensor da Euna Lee ta Sashen Koriya ta Muryar Amurka da babban editan Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha suka yi jawabi
Ana shirye-shiryen jana’izar tsohuwar matar Nelson Mandela, Winnie, wacce ta yi fafutukar yaki da tsarin mulkin wariyar launin fata. Ta rasu jiya Litinin tana mai shekaru 81, za a jana’izar a ranar 14 ga watan Afrilu.
Ana ci gaba da jimamin harin Boko Haram da ya kashe mutane 15 a Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Domin Kari