'Yan kasuwa da masu sarafa tumatirin gwangwani sun yaba da matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na hana shigowa da tumatirin gwangwani kasar daga kasashen ketare.
Baicin hana shigowa da tumatirin gwangwani gwamnatin ta kuma kara kudin haraji akan tumatirin da ake shigowa dashi daga ketare.
Gwamnati tace ta dauki matakan ne da zummar karfafa manoman tumatiri na cikin gida tare da taimakawa wadanda suke sarafa timatirin a cikin gida.
Matakin da gwamnati ta dauka ya biyo bayan koke-koken da masu sarafa tumatirin gwangwani suka yi akan yadda tumatirin gwangwanin kasashen ketare ke karya masu tasu kasuwar har ma suka yi barazanar rufe ma'aikatunsu.
Shugaban kamfanin tumatirin gwangwani mafi girma a nahiyar Afirka dake Legas Chief Eric Nwofia yace abun da suke bukata Allah ya biya masu. Yace kukan da suka yi Shugaba Muhammad Buhari ya ji saboda shugaba ne mai son gaskiya.
Alkalumma sun nuna cewa Najeriya na kashe Naira biliyan hamsin da biyu, N52bn, kowace shekara wajen shigo da tumatirin gwangwani kimanin metric ton dubu 150. Lamarin yana hana bunkasar kamfanin cikin gida da manoma.
Su ma manoman tumatirin irinsu Muhammad Rabiu sunce daukan matakin da wamnati tayi yana da kyau. Sun kwatanta da na shinkafa wanda ya taimakawa manomanta.Sun kira manoman tumatir su yi hakuri saboda zasu samu habaka amma kuma su bi doka..
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum