Shugaban yana Magana a jiya lokacin da ya kai ziyara a wani masallacin dake garin Baltimore na jihar Maryland, shugaba Obama ke cewa.
"Mu Amurkawa dukkan mu abu guda muke, amma kuma da zarar wani bangare daga cikin mu ya fara jin cewa ya zama saniyar ware, ko kuma dan bora, ko kuma yana huskantar tsangwama, to wannan alama ce ta cewa kasar na neman shiga cikin wani hali"
Shugaba Obama ya ci gaba da bayani ga taron al’ummar musulmai dake Baltimore, cewa ya damu matuka ga harin da aka kai ga Musulman Amurka, jim kadan da harin da aka kai ga Paris da wanda wasu suka kai a San Bernadino, yace ko wannan masallacin ma ya fuskanci barazanar tashin hankali, ga dai shugaba Obama da abinda yake cewa.
"Sau tari kunsha ganin yadda wasu ke alakanta addini da ta'addanci, wanda hakan bai dace ba, domin ko kwanan nan munji wasu na kalamai wadanda basu dace ba akan musulman Amurka"
Idan dai ba a manta ba dan takaran shugabancin Amurka karkashin tutar jamiyyar Republican Donald Trump, ya bada shawarar cewa ya kamataa dakatar da barin musulmai suna shigowa Amurka har na dan wani lokaci kana a samar da wani kundin tattara bayanai game da musulman dake Amurka ko kuma ya zame dole su shigo kasar, sai dai sauran abokan sa yan takara sunyi fatali da wannan shawara tasa.
Daya daga cikin shugabannin masallacin da Obama ya ziyarta Ba’Amurke amma dan asalin kasar Pakistan Ahmed Rana shi da matar sa sunce sunyi farin cikin cewa shugaba Obama da ‘yar takarar shugaban kasa a karkashin tutar jamiyyar Democrat Hillary Clinton sau tari suna sukan lamirin tsangwamar da ake wa musulmai da musulunci a duniya.