Shugaba Obama ya kai ziyarar ne tare da mataimakin shugaban kasa mai jiran gado Mike Pence, don karfafa 'yan jam'iyyar Republican gwiwa game da manufofin jam'iyyarsu, wanda ya hada da kawo karshen shirin kiwon lafiya din wanda ake kira "Obamacare."
Wadannan tarurrukan biyu na nuni da irin arangamar da ke tafe yayin da fadar White House ke fita daga hannun Obama zuwa hannun shugaba mai jiran gado Donald Trump.
Dokar tsarin saukakakken kiwon lafiyar ta Affordabale Care Act ta samu amincewar Majalisar Tarayyar Amurka a 2010 ne lokacin da 'yan Demorcta ke da rinjaye a Majalisar Dattwa da ta Wakilai da kuma uwa-uba kasancewar Obama, dan Democtart din shi kuma ne Shuganan kasa. To amma daga ranar 20 ga wannan wata na Janairu, wanda tarin ikon zai koma ne ga 'yan Republican.
Trump ya bayya tsarin na Obamacare da "shirme" wanda ke kuma cike da tsada, kuma a yayin da bai bayyana takamaiman yadda zai maye gurbin tsarin ba, ya bayyana a fili cewa zai kawo karshensa.