Kamar yadda wani rahoto da ya fito daga ofishin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna a ranar Juma’a, ya nuna cewa, an sami rototon cin zarafin na saduwa har guda 99 inda ya wuce na shekarar 2014 da aka sami rahoton 80.
Yawancin zarge-zargen sun fito ne daga ko dai inda sojojin da ‘yan sandan kiyaye zaman lafiyar na MDD suka gama aiki ko kuma wajen da suke kan aikin kawo zaman lafiyar.
Wani karamin Sakataren ayyukan majalisar Atul Khare yace, ba zamu yarda da irin wannan aika-aikar ba, ta kyale wadanda ya kamata su kare al’umma kuma su zama sune dodanninsu ba.