Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Almundahana: EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Shuguban NHIS, Usman Yusuf


Farfesa Usman Yusuf
Farfesa Usman Yusuf

Ana zargin tsohon shugaban hukumar NHIS ne da yin amfani da mukami wajen baiwa kansa damar da ba ta dace ba tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta gurfanar da tsohon shugaban hukumar inshorar lafiyar Najeriya (NHIS), Usman Yusuf, a bisa sabbin tuhume-tuhume 5, dake da nasaba da zamba.

An gurfanar da Usman Yusuf ne a gaban mai shari’a Chinyere Nwecheonwu na babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja.

Wanda ake tuhumar ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa akai sa’ilin da aka karanto masa su.

Ana zargin tsohon shugaban hukumar NHIS ne da yin amfani da mukami wajen baiwa kansa damar da ba ta dace ba tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.

Haka kuma ana zarginsa da ba da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Febrairun da muke ciki, sannan ta ba da umarnin tsare Usman Yusuf a gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja, har sai ta saurari bukatar ba da belinsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG