Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Ta Da Batun Rikicin Gabashin Ukraine Idan Na Hadu da Zelenskiy - Putin

Shugaban Rasha, Vladimir Purtin yayin wata ziyara da ya kai China, ranar 27 ga watan Afrilu, 2019.
Shugaban Rasha, Vladimir Purtin yayin wata ziyara da ya kai China, ranar 27 ga watan Afrilu, 2019.

Yayin da yake magana a wata ziyarar da ya kai China a jiya Asabar, Putin ya ce, yana so ya san fahimci matsayar zababben shugaba, Volodymr Zelensky kan rikicin.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce zai tattauna kan batun rikicin gabashin Ukraine, idan har za su hadu da sabon shugaban kasar.

Yayin da yake magana a wata ziyarar da ya kai China a jiya Asabar, Putin ya ce, yana so ya san fahimci matsayar zababben shugaba, Volodymr Zelensky kan rikicin.

A cewar shugaba Putin, al’umar kasar ta Ukraine sun gaji da wannan rikici.

Ya kuma kara da cewa, gwamantinsa na tunanin bai wa dukkan ‘yan kasar ta Ukraine damar zama ‘yan kasa.

A ranar 4 ga watan Afrilu, Putin ya sa aka sassauta matakan zama dan kasa ga mazauna yankunan Donestk da Luhanks da ke kasar ta Ukraine, matakin da ya sha suka daga tarayyar turai da Amurka da Birtaniya da sauran kasashe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG