“Wannan filin jirgin sama, bashi da amfani. Domin yanzu tun da aka tashi tafiya Hajji, ba’a kara amfani da shi ba, sai da gwamna ya dawo. Wannan ba bukatar mutanen Jigawa bace, wannan bukata ce ta gwamnan Jihar Jigawa. Kamar mu a jam’iyyar APC, ina tabbatarwa idan muka samu gwamnati, samu sayar da wannan filin jirgin sama”, Faruk Adamu Aliyu kennan, jigo a cikin Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, kuma mai neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna a Jihar.
Tuni Jam’iyyar PDP wadda gwamnatinta ce ta gida filin jirgin saman a dutse ta mayar da martani game da kalamun APC.
Alhaji Salisu Mamuda shine shugaban PDP a Jihar Jigawa “Airport ana ce mata ‘Dutse International Airport’, ba ‘Dutse State Airport’ ba. Wannan tasha, gwamnatin Tarayya zata biya mu kudinmu da muka kashe baki daya, domin ayi amfani da su wajen yiwa talakawan Jigawa wani aiki na cigaba.”
Ranar Talata ne akayi bukin bude wannan sabon tashar Jirgi.