Aikin gina filin ya lankwame kimanin nera biliyan goma sha biyar. Duk da kudin da jihar ta kashe nera miliyan dari bakwai da hamsin kacal ya shiga hannun jihar daga gwamnatin tarayya.
Shugaba Goodluck Jonathan ya yabawa gwamna Lamido bisa wannan abun tarihi da ya gina. Sai dai game da kudaden aikin kuwa shugaba Jonathan yace gwamnatin tarayya zata tallafawa jihar da kudade masu tsoka amma fa ba duka zata biya ba. Haka kuma shugaban na Najeriya ya sanarda al'ummar Jigawa cewa "zamu cigaba aiki da gwamnanku mai hangen nesa domin kawo abubuwan alfanu da dimokradiya take haifarwa".
'Yan Jigawa sun fadi albarkacin bakinsu. Wani daga Ringim yace wannan shi ne babban abun farin ciki ga mutumin Jigawa domin abun da ake gani a kasashen duniya yau gashi ya zo har kauyensu ya samesu. Musamman bana an yi aikin hajji. Babu wani alhaji daga jihar da ya zo ya kwana a sansanin alhazai. Kai tsaye da zuwansa Dutse sai shiga jirgi.
Muhammed Badamasi daga Birnin Kudu yace babu abun da zasu maimaita banda godiya saboda abubuwa ne da basu taba gani ba kuma basu taba tunanensu ba a rayuwarsu. Ya yiwa gwamna Sule Lamido uban taron addu'ar Allah ya tabatar masa da abun da yake so.
Su ma dattawan Jigawa sun sha alwashin cigaba da bada gudummawar gina jihar kamar yadda Alhaji Umar Musa Zandam shugaban kwamitin dattawan jihar ya fada. Wannan gwamnatin ta yadda zata yi aiki da dattawa kuma tayi dasu iyakar gwargwado. Idan kuma wadda ta gajeta ta kuduri aniyar yin aiki dasu zasu bada shawara. Yace amma shi dattijon kirki ba zuwa yake yi yace ya bayar da shawara kaza da kaza da aka dauka ko kuma ba'a dauka ba.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.