Majalisun kasar Najeriya suna kokarin yiwa kundun tsarin mulkin kasar gyaran fuska.
An dade ana kokarin gyaran kundun tsarin mulkin. A majalisun baya an yi irin wannan yunkurin. An so a yi gyara akan baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kansu.
A wannan karon maganar 'yancin kananan hukumomi ta sake kunno kai. Majalisar waikilai ta amince da haka. Majalisar dattawa ita ma ta amince da baiwa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu amma bata amince da batun cirewa shugaban kasa da gwamnoni kariya ba, maganar dake hade da na kananan hukumomi. Wannan ya nuna akwai rashin jituwa tsakanin majalisun biyu.
Idan har majalisun basu yadda akan kowace irin magana ba zata yiwu ba a mika maganar ga majalisun jihohi. Domin dole sai da amincewar majalisun jihohi za'a iya yiwa kundun tsarin mulki gyaran fuska ta kuma zama dokar kasa.
Akan ko za'a iya yin gyaran kafin a yi zaben shekara mai zuwa wakiliyarmu tace zai yi wuya a samu dokar ta tabbata kafin zaben. Babu yadda dokokin zasu kai jihohi a yi muhawara akansu kana su zama doka cikin watanni uku da suka saura kafin a yi zabe.
To saidai bayan zabe za'a cigaba da maganar a sabbin majalisun dake zuwa.
Ga karin bayani.