Sakamakon ra’ayoyin jama’a a jiya Laraba ya nuna cewa jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Firai minista David Cameron ta sami goyon baya da kashi 33 daga cikin dari na masu kada kuri’ar Britaniya.
Ita kuma babbar jam’iyyar adawa ta Ed Milliband na bayanta da maki daya.
Ra’ayoyin na jama’a sun nuna cewa sakamakon zaben ka iya tilasta daya daga cikin manyan jam’iyyun kasar guda biyu kafa gwamnatin kawance da wata daga cikin sauran jam’iyyun da basu da kujeru da yawa a majalisar mai kujeru 650.
Masu nazari sun ce wannan zaben na Britaniya shine mafi wuyar hasashe da aka taba gani kuma yana da muhimmanci.