Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN NIJAR: Mahaman Ousman Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hukuncin Kotun Tsarin Mulki


Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar
Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar

Dan takarar jam'iyyar RDR Canji da kotun tsarin mulkin Nijar ta bayyana a matsayin wanda ya fadi a zaben shugaban kasar Nijar na ranar 21 ga watan Fabrairu Alhaji Mahamane Ousmane ya bayyana matsayarsa kan hukunci da kotun ta yanke.

Dantakar ya kuma kudiri aniyar ganin an mayar masa da amanar da ya ce talakawa suka ba shi a yayin fafatawar da suka yi da Bazoum Mohamed.

Dandazon magoya bayan jam’iyyun kawancen adawa sun yi wani gamgami da daren Litinin 22 ga watan Maris a kofar gidan Alhaji Mahamane Ousmane​ da ke birnin Yamai, inda suka shafe wuni suna jiran jin matsayinsa a game da sakamakon din-din-din din da kotun tsarin mulkin kasa ta fitar a cikin daren ranar Lahadi 21 ga watan Maris.

Karin bayani akan: Mahamadou Issouhou, CENI, Mahamane Ousmane, da Nijar.

Bayan wata doguwar tantaunawa da abokan tafiyarsa na CAP 2021 da ACC da FRC, dan takarar na jam’iyar RDR Canji ya gana da manema labarai domin sanar da duniya cewa, bai yarda da sakamakon da ya bayyana shi a matsayin wanda ya sha kasa ba, domin a cewarsa, yana da kwarin guiwa a kan cewa shi talakawa suka zaba a yayin zagaye na 2 na zaben watan Fabrairu da ya gabata.

A cikin bayaninsa, Mahamadou Issouhou ya ce kotun tsari mulki ta Nijar ta yi gaggawa tun da yana da dama har zuwa ranar 26 ga watan Maris amma a ranar 21 ga watan na Maris akai maza aka fitar da sakamakon zabe saboda a farantawa wasu rai, kuma ba a basu damar su kawo amsa bisa amsar da abokan hamaryarsu su ka yi bisa karar da su ka shigar ba.

Sannan kuma bayan haka akwai wadanda su ka yi sheda a cikin rumfunan zabe wanda su ne ya kamata ace an saurara a samu hujjoji masu karfi kuma da ra’ayinsu ba’a saurare su ba yadda ya kamata.

Ya kuma yi kira ga dukan ‘yan Nijar da su tashi tsaye su yi tsayin daka bisa kan shirya jerin gwano don ganin cewa, duniya ta san halin da ake ciki kuma suna so a yi shi a duka jihohin Nijar gaba daya.

Da yake bayani jim kadan bayan kotun tsarin mulkin kasa ta tabbatar da shi a matsayin sabon zabeben shugaban kasa, dan takarar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed ya bukaci samun hadin kan Mahaman Ousman, mutumin da ya kira mai halin dattako.

Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Sai dai wasu alamu na nuni da cewa, magoya bayan jam’iyyun adawa na cikin yanayin fusata a yanzu haka domin ko a ranar Litinin ma an dan fuskanci tashin tarzoma a wasu sassan birnin Yamai, ko da yake bai je ko ina ba jami’an tsaro suka ci karfin abin.

Kotun, wacce ta zauna a yammacin ranar Lahadi 21 ga watan Maris, ta ce Bazoum zai karbi ragamar mulki daga ranar 2 ga watan Afrilu domin fara wa’adinsa na shekara biyar.

Hakan na nufin wa’adin shugaba mai barin gado Mahamadou Issouhou zai kare a ranar bayan kammala wa’adinsa na biyu na shekara biyar-biyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Kotun tsarin mulkin kasar, ita take da hurumin ayyana sakamakon zabe a mataki na karshe, duk da cewa hukumar zabe ta CENI, ta fitar da alkaluman da suka nuna dan takarar da ya lashe zaben a baya.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG